✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashawa: Tushen ruguza zaman lafiya da yada fasadi (1)

Huduba ta Farko Godiya ta tabbata ga Allah Masani, Mai hikima, Mafi kwarewa a halitta, kuma Mafi hikima a shari’a, maganarSa ta kasance gaskiya ce,…

Huduba ta Farko

Godiya ta tabbata ga Allah Masani, Mai hikima, Mafi kwarewa a halitta, kuma Mafi hikima a shari’a, maganarSa ta kasance gaskiya ce, hukuncinSa kuma adalci ne. “Kuma kalmar Ubangijinka ta cika, tana gaskiya da adalci. Babu mai musanyawa ga kalmominSa, kuma Shi ne Mai ji, Masani.” (k:6:115). Muna gode maSa a bisa datarwarSa da shiryarwarSa, muna yi maSa shukura a bisa kariyarSa da kularSa gare mu.

Na shaida babu wanda ya cancanci bauta sai Allah, Shi kadai ba Ya da abokin tarayya a gare Shi. Idan mutane suka yi hukunci da shari’arSa sai su shiryu kuma su samu zaman lafiya, idan kuma suka yi hukunci da shari’ar waninSa sai su shiga firgici kuma su tabe. “Da wadansu abubuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da kasa) baya ga Allah, hakika da su biyun sun baci. Saboda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al’arshi daga abin da suke siffantawa.” (k:21:22). Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, Ubangijinsa Ya yi masa magana da cewa: “Sa’an nan Muka sanya ka a kan wata shari’a ta al’amarin. Sai ka bi ta, kuma kada ka bi son zuciyoyin wadannan da ba su sani ba. Lallai ne su, ba za su wadatar da kai da komai ba daga Allah. Kuma lallai ne azzlumai, sashinsu majibintan sashi ne, kuma Allah ne Majibincin masu takawa.” (k:45:18-19). Don haka sai (SAW) ya kwatanta bin UbangijinSa, kuma ya bi shari’arSa, ya yi kira zuwa gare ta, ya yi gwagwarmaya da mutane a kanta har Allah Ya amshi ransa, tsira da aminci da albarkar Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa da masu binsa har zuwa Ranar Sakamako.

Bayan haka, ku ji tsoron Allah Madaukaki, ku yi maSa da’a, ku yi aiki na kwarai don ku hadu da Shi lami lafiya. Ku kiyayi kudin haram, domin shi bala’i ne a kan ma’abucinsa. Kudin haram kazanta ce da ake azabtar da bawa kanta a Lahira. Duk jikin da ya ginu da kazanta to wuta ce ta fi dacewa da shi. “Kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da karya, kuma ku sadu da ita zuwa ga mahukunta domin ku ci wani yanki daga dukiyoyin mutane da zunubi, alhali kuwa ku, kuna sani.” (k:2:188).

Ya ku mutane! Allah Ya halifantar da mutane a bayan kasa, Ya sallamar musu da jagorancinta, Ya huwace musu dukkan abubuwan halittta, mutane suna nome kasa, suna nike duwatsu sun shige cikin sahara suna amfanarta, suna shimfida hanyoyi suna yi nutso a cikin tekuna fiye da kifaye.

An huwace musu dabbobi suna yi musu hidima, sun cimma tsuntsu a sararin samaniya har suka ketare shi a tashi. Miyagun dabbobin daji suna tsoronsu, su kuma (mutanen) ba su tsoronsu. Sai ya zamo dan Adam ba ya jin tsoron komai a bayan kasa face dan uwansa dan Adam. Domin haka ne Allah Ya shar’anta shar’o’i saboda a kiyaye hakkoki a tsarkake rayuka a daidaita al’amura a kuma tabbatar da zaman lafiya. Kowane daya daga cikin mutane ya san hakkinsa da hakkin da ke kansa. Kada ya yi sakaci da hakkinsa kuma kada ya yi ta’addanci a kan waninsa. Idan mutane suka yi hukunci da shari’ar Allah Madaukaki, sai cikakkiyar zaman lafiya da yalwataccen arziki su tabbata a gare su. Kuma zaman lafiyarsu da arzikinsu za su nakasa ne gwargwadon yadda suka karkace daga shari’ar Allah Madaukaki. 

Lallai tsoro da firgici suna samuwa ne sakamakon kauce wa shari’ar Allah gaba dayanta ko wani bangarenta. Idan tsoron Allah ya yi rauni a zuciyar bawa, sai ya shiga aikata zalunci da fasadi, idan bai ji gargadi kan ukuba ba, sai ya rika ta’addanci a kan sauran jama’a yana zaluntar mutane yana cin hakkokinsu.

Don haka tu’ammali da rashawa kofa ce ta yaduwar fasadi, kuma cuta ce da sharri da bala’i. Cin hanci da rashawa da almundahana na jawo bala’o’i da masifofi ga mutum a shi kadai da kuma jama’a baki dayanta. Kuma rashawa tana bata addini, tana rusa amana, tana yada ha’inci, tana daukaka mafiya kaskancin mazaje, kuma tana rusa musu mutuncinsu!    

Ba za a samu tabbataccen zaman lafiya da arziki a cikin kasa ko al’ummar da rashawa ta watsu a cikinta ba, maimakon haka sai tsoro da rashin zaman lafiya da talauci da yunwa su mamaye ta. Hakika kuma talauci abokin gaban zaman lafiya ne, kuma lallai yunwa tana jawo rashin zaman lumana. Sanannen abu ne cewa, talauci yana yaduwa ne sakamakon yaduwar rashawa da almundahana, domin masu cin hanci da rashawa ko almundahana suna rike hakkokin mutane su hana su abubuwan jin dadin rayuwa har sai sun ba su rashawar ko sun wawuri abin da suke so, sai dukiyar masu cin rashawar ta karu, a lokacin da da’irar talauci ke fadada a tsakanin jama’a.

Idan kwararru da masu zuba jari suka ga ana kokarin lalata musu harkoki saboda mujirimancin masu karbar rashawa, sai su bar kasashensu su watsu kasashen da rashawarsu kadan ce su rika aiki a can, sai dukiyoyinsu su rika bunkasa. Hakika kwararru da masu zuba jari da yawa sun yi hijira zuwa kasashen Yammacin Turai, saboda a kasashensu na asali ba a ba su matsayin da ya dace da su. Kuma ba su iya gudanar da ayyukansu sai da kwararrun abokan hadin gwiwa ko da bayar da babbar rashawa, sai kasashen da rashawa ta mamaye suka rika ci baya, babu saura a cikinsu face barayin gwamnati da masu karbar rashawa sai kuma wadanda aka zalunta aka fi karfinsu, wadanda illar rashawar take kai su bango, su rika tunanin daukar makami ko bore don samun wani juyin juya-hali saboda nemo mafita.

Duk wani mai hankali ya san abin da ya faru ko yake faruwa a kasashen Larabawa na bore da juyin juya-hali na faruwa ne saboda an kai mutane bango ta yadda suka yanke kauna daga gyaruwar al’amura. Zalunci ya watsu a cikinsu sosai, rashawa ta yadu a cikinsu kamar wutar daji har ta ci karfin mutane, ta lalata harkokinsu, mutane sun koma suna neman dukiya ce ga wasu ’yan kalilan din mutane masu karfi da suke ba su dan albashi cikin cokali, suke zaluntarsu suna hana su hakkokinsu sai sun ba da rashawa ga wadanda suka ginu kan cin dukiyar mutane da zalunci!

Lallai rashawa tana shuka gaba da kiyayya a zukatan mutane, sai masu rauni su rika jin haushin masu karfi, talakawa su rika jin haushin masu dukiya, sai al’umma ta rabu gida biyu masu gaba da juna. A rasa zaman lafiya da kwanciyar hankali, tsoro da tashin hankali su maye gurabensu.