Masallaci: Ba a fada ba
Fassarar Salihu Makera
HUdUBA TA FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah Masani, Mai hikima, Mafi kwarewa a halitta, kuma Mafi hikima a shari’a, maganarSa ta kasance gaskiya, hukuncinSa kuma adalci ne. “Kuma kalmar Ubangijinka ta cika, tana gaskiya da adalci. Babu mai musanyawa ga kalmominSa, kuma Shi ne Mai ji, Masani.” (k:6:115). Muna gode maSa a bisa datarwarSa da shiryarwarSa, muna yi maSa shukura a bisa kariyarSa da kularSa gare mu.
Na shaida babu wanda ya cancanci bauta sai Allah, Shi kadai ba Ya da abokin tarayya a gare Shi. Idan mutane suka yi hukunci da shari’arSa, sai su shiryu kuma su samu zaman lafiya, idan kuma suka yi hukunci da shari’ar waninSa sai su shiga firgici kuma su tabe. “Da wadansu abubuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da kasa) baya ga Allah, hakika da su biyun sun baci. Saboda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al’arshi daga abin da suke siffantawa.” (k:21:22). Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, Ubangijinsa Ya yi masa magana da cewa: “Sa’an nan Muka sanya ka a kan wata shari’a ta al’amarin. Sai ka bi ta, kuma kada ka bi son zukatan wadannan da ba su sani ba. Lallai ne su, ba za su wadatar da kai da komai ba daga Allah. Kuma lallai ne azzlumai, sashinsu majibintan sashi ne, kuma Allah ne Majibincin masu takawa.” (k:45:18-19). Don haka sai (SAW) ya bi UbangijinSa, kuma ya bi shari’arSa, ya yi kira zuwa gare ta, ya yi gwagwarmaya da mutane a kanta har Allah Ya amshi ransa. Tsira da Aminci da albarkar Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa da masu binsa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah Madaukaki, ku yi maSa da’a, ku yi aiki na kwarai don ku hadu da Shi lami lafiya. Ku kiyayi kudin haram, domin kudin haram bala’i ne a kan ma’abucinsa. Kudin haram kazanta ne da ake azabtar da bawa a kansa a Lahira. Duk jikin da ya ginu da kazanta, to wuta ce ta fi dacewa da shi. “Kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da karya, kuma ku sadu da ita zuwa ga mahukunta domin ku ci wani yanki daga dukiyoyin mutane da zunubi, alhali kuwa ku, kuna sani.” (k:2:188).
Ya ku mutane! Allah Ya halifantar da mutane a bayan kasa, Ya sallamar musu da jagorancinta, Ya huwace musu dukkan abubuwan halittta, mutane suna nome kasa, suna nike duwatsu sun shige cikin sahara suna amfanarta, suna shimfida hanyoyi suna yi nutso a cikin tekuna fiye da kifaye.
An huwace musu dabbobi suna yi musu hidima, sun cimma tsuntsu a sararin samaniya har suka ketare shi a iya tashi. Miyagun dabbobin daji suna tsoronsu, su kuma (mutanen) ba su tsoronsu. Sai ya zamo dan Adam ba ya jin tsoron komai a bayan kasa face dan uwansa dan Adam.
Domin haka ne Allah Ya shar’anta shar’o’i saboda a kiyaye hakkoki, a tsarkake rayuka, a daidaita al’amuran rayuwa, kuma a tabbatar da zaman lafiya. Kowane daya daga cikin mutane ya san hakkinsa da hakkin da ke kansa. Kada ya yi sakaci da hakkinsa kuma kada ya yi ta’addanci a kan na waninsa.
Idan mutane suka yi hukunci da shari’ar Allah Madaukaki, sai cikakkiyar zaman lafiya da yalwataccen arziki su tabbata a gare su. Kuma zaman lafiyarsu da arzikinsu za su nakasa ne gwargwadon yadda suka karkace daga shari’ar Allah Madaukaki. Lallai tsoro da firgici suna samuwa ne sakamakon kauce wa shari’ar Allah gaba dayanta ko wani bangarenta. Idan tsoron Allah ya yi rauni a zuciyar bawa, sai ya shiga aikata zalunci da fasadi, idan bai ji gargadi kan ukuba ba, sai ya rika ta’addanci a kan sauran jama’a yana zaluntar mutane yana cin hakkokinsu.
Don haka tu’ammali da rashawa kofa ce ta yaduwar fasadi, kuma cuta ce da sharri da bala’i. Cin hanci da rashawa da almundahana na jawo bala’o’i da masifofi ga mutum a kashin kansa shi kadai da kuma jama’a baki dayanta. Kuma rashawa tana bata addini, tana rusa amana, tana yada ha’inci, tana daukaka mafiya kaskancin mutane, kuma tana rusa musu mutuncinsu!
Ba za a samu tabbataccen zaman lafiya da ingantuwar tattalin arziki a cikin kasa ko al’ummar da rashawa ta watsu a cikinta ba, maimakon haka sai tsoro da rashin zaman lafiya da talauci da yunwa su mamaye ta. Hakika kuma talauci abokin gaban zaman lafiya ne, kuma lallai yunwa tana jawo rashin zaman lumana. Sanannen abu ne cewa, talauci yana yaduwa ne sakamakon yaduwar rashawa da almundahana, domin masu cin hanci da rashawa ko almundahana suna rike hakkokin mutane ne su hana su abubuwan jin dadin rayuwa har sai sun ba su rashawar ko su wawuri abin da suke so daga dukiyar kasa, dukiyar masu cin rashawar ta karu, a lokacin da da’irar talauci ke fadada a tsakanin jama’a.
Idan kwararru da masu zuba jari suka ga ana kokarin lalata musu harkoki saboda mujirimancin masu karbar rashawar, sai su bar kasashen su koma kasashen da rashawarsu kadan ce su zuba jari a can, sai dukiyoyinsu su rika bunkasa. Hakika kwararru da masu zuba jari da yawa sun yi hijira zuwa kasashen Yammacin Turai ne, saboda a kasashensu na asali ba a ba su matsayin da ya dace da su. Kuma ba su iya gudanar da ayyukansu sai da kwararrun abokan hadin gwiwa ko da bayar da babbar rashawa, sai kasashen da rashawa ta mamaye suka rika ci baya, babu saura a cikinsu face barayin gwamnati da masu karbar rashawa, sai kuma wadanda ake zalunta da aka fi karfinsu, wadanda illar rashawar take kai su bango su rika tunanin daukar makami ko bore don samun wani juyin juya-hali saboda neman mafita.
Duk wani mai hankali ya san abin da ya faru ko yake faruwa a kasashen Larabawa da sauran kasashe na bore da tashin hankali na faruwa ne saboda an kai mutane bango ta yadda suka yanke kauna daga gyaruwar al’amura. Zalunci ya watsu a cikinsu sosai, rashawa ta yadu a cikinsu kamar wutar daji har ta ci karfin mutane, ta lalata harkokinsu, mutane sun koma suna neman dukiya ce ga wadansu ’yan kalilan din mutane masu karfi da suke ba su dan albashi cikin cokali, suke zaluntarsu suna hana su hakkokinsu sai sun ba da rashawa ga wadanda suka ginu kan cin dukiyar mutane da zalunci!
Lallai rashawa tana shuka gaba da kiyayya a zukatan mutane, sai masu rauni su rika jin haushin masu karfi, talakawa su rika jin haushin masu dukiya, sai al’umma ta rabu gida biyu masu gaba da juna. A rasa zaman lafiya da kwanciyar hankali, tsoro da tashin hankali kuma su maye gurabensu.
Idan rashawa ta kai kololuwa a cikin kasa, manyanta suka koma maciya rashawa da tafka almundahana, sai martabarsu da girmansu su fadi a idon talakawa, jama’a su rika kyamarsu, amincin da ke tsakanin jama’ar kuma ya lalace. Sai a wayi gari babu mai kyamar rashawa sai wanda addini yake tsoratar da shi, ko muru’arsa ta hana shi. Hakika mutane sun sani kuma sun ji labarin kasashen da rashawa ta kai har ana dabdala da ita a tsakanin ministoci zuwa sama, har ya zamo kudin rashawar da mai ba da rashawar zai mika tana bin hannunwa da dama na ma’aikata kafin ta isa hannun babba. To duk lokacin da hannuwan kaiwa suka yi yawa, sai rashawar ta karu, a rika kare masu ba da ita, ta yi ta yawaita, sai fasadinta ya karu, kasa ta zama kamar ribatacciyar yaki, mutane su rika fada har kasar ta rikice, mutanenta su shiga tashin hankali.