✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha za ta dandana kudarta muddin ta mamaye Ukraine – Amurka

Amurka ta ce ta tanadi matakan karya tattalin arziki kan Rasha, muddin ba ta janye aniyarta ba.

Amurka ta gargadi kasar Rasha da cewar za ta dandana kudarta muddin ta kuskura ta mamaye kasar Ukraine, kamar yadda alamunta ke nunawa.

Wani jami’i a Sashen Harkokin Waje na Amurka, Derek Chollet, ne ya yi gargadin ranar Lahadi, inda ya ce kasarsa za ta kakaba wa Rashar takunkumin karya tattalin arziki in ba ta janye jikinta daga mamayar Ukraine din ba.

Gargadin na zuwa ne bayan wani kiran waya kan takaddamar tsakanin Shugaba Vldimir Putin na Rasha da takwaransa na Amurka, Joe Biden, ya kare ba tare da cimma wata matsaya ba.

Fadar White House dai ta ce yin kashedin ya zama wajibi la’akari da kunnen uwar shegun da Rasha ke ci gaba da yi kan kiraye-kirayen kasashen duniya a kan lamarin.

A wani labarin kuma, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken, ya ce barazanar ta Rasha ta isa ta zama dalilin da zai sa ma’aikatan huldar jakadanci su fice daga birninta na Kyiv, ko da yake ya ce har yanzu bai yanke kaunar cewa za a sami sulhu ta hanyar diflomasiyya ba.

“Har yanzu kofar sulhu a bude take. Hanyar da Rasha za ta bi don tabbatar da hakan mai sauki ce; kawai ta ja da baya, ba wai ta ci gaba da mamaya ba,” inji Mista Blinken.