Kasashen Turai sun shiga fargaba bayan Rasha ta rufe katafaren bututun iskar gas din da take tura musu ta na tsawon kwana 10.
Rasha ta ce ta rufe bututun — mai suna Nord Stream 1 — ne daga ranar Litinin domin gudanar da gyare-gyare a kansa a tsawon lokacin, amma Jamus na zargin da wuya ta sake budewa.
- Yadda hukumomin Saudiyya ke ‘wulakanta’ Alhazan Najeriya
- NAJERIYA A YAU: ‘Yadda na yi kundumbalar ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna’
Ministan Tattalin Arzikin Jamus, Robert Habeck, ya ce matakin da Rasha ta dauka, “Ya jefa mu cikin wani garari da ba mu taba shiga ba, komai na iya faruwa,” kamar yadda ya shaida wa wani gidan rediyon kasar sa a karshen mako.
A ranar 21 ga watan Yuli ne dai ake sa ran Rasha za ta sake bude bututun Nord Stream 1, wanda ta shi kasashen Turai ke samun mafi yawan iskar gas din da suka godara da ita a matsayin makamashi.
Sai dai kuma a baya wasu aikin gyare-gyaren da aka yi a kan katafaren bututun sun wuce wa’adin da aka dibar musu.
Kasashen Turai sun dogara da Rasha wajen samun iskar gas din da suke bukata, wanda kuma take turawa kai-tsaye zuwa Jamus.
Sai dai kuma bayan Rasha ta afka wa makwabciyarta Ukraine da yaki a bana, Jamus ta rage yawan iskar gas din da take saye daga wurinta zuwa kashi 35 daga kashi 55 cikin 100.
Matakin, Jamus da sauran kasashen Yammacin duniya sun dauka ne domin karya gurgunta Gwamnatin Shugaba Valdimir Putin ta fuskar tattalin arziki.