Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin, ya ce yana son a yi zama gaba-da-gaba tsakaninsa da takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelensky, domin kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin da kasashen biyu ke yi.
Kasar Turkiyya, wadda take shiga tsakani domin sasanta Rasha da Ukraine, wadanda makwabtan juna ne, ita ce ta sanar da sharuddan da Rasha ta gindaya.
- Masu son kawo rikici a zaben 2023 su kuka da kansu —Sojoji
- Buni ya sa labule da shugabannin taron APC —Buni
Wannan na zuwa ne bayan tattaunawar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya yi da Mista Putin ta wayar tarho.
Alamu na nuna cewa jagorantar sulhun da Shugaba Erdogan ya yi na iya haifar da kyakkyawan sakamako a karshe.
– Sharuddan da Rasha ta kafa –
Sharuddan na Rasha sun kasu kashi biyu: kashin farko na kunshe da jerin abubuwa hudu masu sauki ga Ukraine ta cika; kashi na biyun kuma na cike da sarkakiya.
Masu sauki
Rasha ta ce dole ne Ukraine ta daina kowane irin yunkuri na shiga kungiyar tsaro ta NATO, kuma tuni Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ba da kai bori ya hau.
Sauran sharuddan sun wajabta wa Ukraine rabuwa da makaman da za su zama barazana ga Rasha.
Tilas ne a tabbatar da kare harshen Rasha da kuma kawar da akidun ’yan Nazi a cikin Ukraine.
Sai dai wannan sharadi zai iya kasancewa kullutu a wuya ga Ukraine, wadda shugaban nata Bayahude ne.
Amma duk da haka Turkiyya na kai gwauro tana kai mari kan sharudan da Rasha ta gindaya don ganin an samu maslaha.
Sharudda masu sarkakiya
Kashi na biyu na bukatun na Rasha da ke da sarkakiya sun hada da;
Na farko Putin yana son tattaunawa gaba-da-gaba da Zelensky, kafin cimma duk wata yarjejeniya.
Rasha na so Ukraine ta hakura da yankin Donbass da ke Gabasinta, wanda ya balle daga Ukraine ya koma cikin Rasha.
Sai dai kuma abu ne mai wuyar gaske Ukraine ta hakura da wannan yanki.
Karfa-karfa
Wasu masana harkar tsaro na ganin wadannan sharuda da Rasha ta gindaya ba komai ba ne face karfa-karfa a kan Ukraine.
A cewarsu hakan na iya zame wa Ukraine barazana a nan gaba domin wani shugaban na iya amfani da yarjejeniyar wajen sake mamayar kasar a nan gaba.
Har wa yau, ana hasashen cewa yarjejeniyar na iya daukar tsawon lokaci kafin a cimma matsaya, ga shi kuma ita Ukraine na ci gaba da tafka asarar rayuka da dukiya mai tarin yawa.