✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha ta harba wa Ukraine makamai masu linzami 600

Kashi 95 cikin 100 na sojojin kundunbalan Rasha sun shiga Ukraine da yaki

Rasha ta harba makamai masu linzami akalla  guda 600 a cikin kwana 10 da ta far wa Ukraine da yaki.

Wani babban jami’in ma’aikatar tsaron Amurka ya bayyana cewa kawo yanzu, kashi 95 cikin 100 na sojojin kundunbalan Rasha sun shiga Ukraine da yaki.

Da yake bayani a ranar Lahadi da yakin ke ciwa kwana 10 da farawa, ya ce an ci gaba da yaki a biranen Kherson da Mykolaiv a yayin da dakarun Rasha ke kokarin su yi wa biranen Kyiv, Khakhiv, Chernihiv da kuma Mariupol, kofar rago.

Amma ya bayyana cewa yunkurin sojojin ya gamu da turjiya daga bangaren Ukraine.

Kayan yakin Rasha na kan hanya

A bangare guda kuma, jerin gwanon motoci da makamai da dakaru mai stawon kilomita 70 da Rasha ta tura zuwa Ukraine ya ci karo da cunkoson da ya hana shi tafiya gaba.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu bayani game da tazarar da ke tsakanin jerin gwanon kayan yakin da Kyiv, babban birnin Ukraine.

A makon da ya gabata dai tarazar makaman zuwa tsakiyar birnin Kyiv bai wuci kilomita 25 ba.

Yaki a sararin samaniya

Har yanzu dai ana ci gaba artabu tare da kokarin kwace ikon sararin samaniyar kasar Ukraine tsakanin sojojin Rasha da na Ukraine inda kowane bangare ke da kaso mai tsoka na makamai da jiragen yaki da ke shawagi.

“Mun yi amannar cewa har yanzu yawancin sassan Ukraine na amfani da hanyoyin sadarwa da intanet da kafafen yada labarai,” a cewar jami’in na Amurka.

Ya kara da cewa a yankin Odessa kuma, an kai hari ta ruwa.

Sai dai ya ce ba su da tabbaci game da rahoton da ke zargin sojojin Rasha da bude wuta kan masu zanga-zanga a birnin Kyiv.