Ma’aikatar Tsaron kasar Rasha ta tabbatar da cewa dakarunta ne suka kai harin makami mai linzami zuwa tashar jirgin kasa da ke Kyiv babban birnin kasar Ukraine ranar Laraba.
Ma’aikatar ta kuma ce harin dai ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 25, da suka hada da sojoji da fararen hula.
Kakakin ma’aikatar tsaron, Igor Konashenkov, ya yi ikirarin cewa sama da sojojin Ukraine 200 da ke kan hanyarsu ta zuwa yaki yankin Donbass, su ma sun mutu a garin Chaplyne da ke tsakiyar yankin Dnipropetrovs a sanadiyar harin.
Babu wata shaida dai da ta tabbatar da ikirarin.
Konashenkov ya kara da cewa, makamin rokar ya afka wa wani bangare na tashar da sojojin Ukraine ke amfani da su, sannan an lalata kayan yakin sojojin kasar.
A hannu guda kuma hukumomin Ukraine sun ce mutane 25 da suka hada da kananan yara biyu ne suka mutu a harin, yayin da wasu 30 suka jikkata.
Mataimakin shugaba a ofishin shugaban kasar Ukraine Kyrylo Tymoshenko, ya bayyana cewa sojojin Rashan sun kai hari dukkanin unguwani da kuma hanyoyin jirgin kasa da ke yankin Chaplyne.
Ya ce wani yaro mai shekara 11 ya mutu sakamakon ginin da ya fado masa, sai kuma wani mai shekara da wutar da ta tashi a kusa da tashar jirgin kasa, duk sanadiyar harin.
Sai dai wadannan bayanai na banarorin biyu, babu wani ma`aunin da zai tabbatar ko kore su.