Gwamnatin Rasha ta bayar da umarnin kammala gyarna gadar saman da aka kai wa hari a bom a karshen mako cikin wata bakwai.
Fira Minista Mikhail Mishustin ya bayar da umarni a safiyar Juma’a na kammala aikin gyaran gadar da ta hada kasar da yankin Crimea kafin ranar 1 watan Yuli na 2023.
- An tsinci gawar mace da aka yi gunduwa-gunduwa da ita a Indiya
- Dubun ’yan kasuwa masu garwaya takin zamani da yashi ta cika a Jigawa
- NAJERIYA A YAU: ‘Mu ke da alhakin sayen audugar Al’adar ’ya’yanmu’
A ranar Asabar ne aka kai harin bom a gadar, wadda ke dauke da layin jirgin kasa da tituna, wadda kuma aka amfani da ita wajen dakon mai ta jirgin kasa daga Rasha zuwa Crimea.
Rasha ta yi zargin abokan gaba ne suka kai mata harin, wanda daga bisani ta tsananta kai munanan hare-hare kan makwabciyarta, kasar Ukraine da suke yaki.
Kimanin wata 10 ke nan da kasashen biyu ke yakar juna tun daga ranar 23 ga watan Disamban 2021.
Mamayar ta Rasha dai ta yi ajalin dubban mutane da baya ga asarar dukiyoyi da raunata mutane tare da tilasta wa dubban jama’ar Ukraine yin gudun hijira.
Kasashen duniya sun yi tir da harin an Rasha, inda suke bai wa Ukraine goyon baya da gudummawa.