Rasha da Ukraine sun rattaba hannu kan yarjejeniyar bai wa kasashen biyu damar fara fitar da hatsinsu zuwa kasuwannin duniya.
Manazarta kan lamuran siyasa na ganin hakan zai taimaka wajen kawo karshen takaddamar da ta janyo barazanar karancin abinci a duniya, a yayin da kasashen biyu ke ci gaba da gwabza yaki a Ukraine.
- Sun yi yunkurin farke cikin kada kan ya hadiye yaro dan shekara 7
- INEC ta cire Mohammed Abacha daga jerin ‘yan takarar Gwamnan Kano
An kulla yarajejiniyar ce a birnin Instanbul na kasar Turkiya a karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma’a.
Tun a makon da ya gabata ne dai wakilan kasashen biyu suka amince da bai wa Kiev kafar fitar da ton miliyan 22 na hatsin da ake bukata cikin gaggawa, da wasu kayayyakin amfanin gona da ke jibge a tekun Bahar Maliya saboda yakin da kasar ta tsinci kanta a ciki da makwabciyarta Rasha.
Ministan Tsaro na Rasha Sergie Shoigu da kuma Ministan Raya Kasa Oleksandr Kubrakov na Ukraine ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnatocinsu.
An gudanar da bikin rattaba hannun ne a Dolmabahce, Fadar gwamnatin Turkiyya, kuma a gaban Shugaba Recep Tayyib Erdogan da kuma Antonio Gutteres, Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya.
A bisa wannan yarjejeniya, Rasha za ta dage takunkumin da ta kakabawa Ukraine na tsawon kwanaki 120, wanda hakan zai isa Ukraine ta fitar da Ton miliyan 25 na alkama da ke dankare a tashar jirgin ruwanta na Odesa.
Rasha ta hana fitar da hatsin ne bisa tsoron amfani da jiragen Ukraine don safarar makamai.
Nigeria ita ce ta hudu a jerin kasashen duniya da ke sayen alkama daga kasar Ukraine, inda alkaluma suka nuna cikinin da kasar ta yi da Ukraine ya kai na Dala miliyan 394.