✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha 2018: Yau Aljeriya da Najeriya za su buga wasan karshe

A yau Juma’a da misalin karfe 9 da rabi na dare agogon Najeriya ne za a buga wasan neman zuwa gasar cin kofin duniya da…

A yau Juma’a da misalin karfe 9 da rabi na dare agogon Najeriya ne za a buga wasan neman zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a badi idan Allah Ya kai mu a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Aljeriya da kuma takwararta ta Super Eagles.  Wasan zai gudana ne a Aljeriya kuma shi ne wasan karshe.  A wasan farko da Najeriya ta yi da Aljeriya a bara, Najeriya ce ta samu nasara da ci 3-1.

Kodayake Najeriya tuni ta samu tikitin tafiya gasar cin kofin duniya a Rasha, amma saboda cika ka’ida ya zama wajibi ta buga wannan wasa na yau.

Wannan wata dama ce da kocin Najeriya Gernot Rohr zai yi amfani da ’yan wasan da ba kasafai suke yi masa wasa ba don ya tantance wadanda zai rika yin amfani da su nan gaba.

Najeriya dai ita ce ke saman teburi a rukunin B inda ta hada maki 13 a wasanni biyar.  Sauran kasashen da ke wannan rukuni sun hada da Zambiya da Kamaru da kuma Aljeriya kuma dukkansu ba su cancanci zuwa gasar ba, don ana daukar kungiya daya ce a kowane rukuni.

Kawo yanzu kasashe biyu ne daga Nahiyar Afirka suka tsallake zuwa gasar cin kofin duniya a Rasha.  kasashe biyun su ne Najeriya da kuma Masar.  Sauran kasashe ukun sai an kammala wasannin da suka rage ne daga yau zuwa ranar Litinin sannan a tantance wadanda suka cancanci shiga gasar.

Wannan tamkar wata dama ce da kocin Najeriya Gernot Rohr zai yi amfani da ita wajen zakulo ’yan kwallon da zai tafi da su gasar cin kofin duniya a Rasha a badi idan Allah Ya kai mu.