Gwamnatin Tarayya ta kudurta aniyar kashewa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles zunzurutun Naira Biliyan 3 a gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a badi idan Allah Ya kaimu.
Ministan Matasa da Wasanni Mista Solomn Dalung ne ya bayyana haka ga menama labarai a ranar Talatar da ta wuce a fadar gwamnati da ke Abuja.
Ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen biyan ’yan kwallon alawus-alawus da ba su horo da kama musu masauki da sauran bukatunsu na yau da kullum.
Ministan ya ce Ma’aikatar matasa da wasanni ta kammala shirye-shiryen aika wata tawaga ta musamman da za ta goya wa Super Eagles baya a yayin gasar a Rasha don karfafawa ’yan kwallon gwiwa.
“Mun yanke shawarar a watan Maris na badi za mu biya dukkan alawus-alawus din ’yan kwallon don karfafa musu gwiwar tunkakar gasar, ba kamar yadda aka rika samun matsala a irin haka a baya ba”, in ji shi.
Super Eagles dai za ta fafata ne a rukunin D da kasashen Ajantina da Kuroshiya da kuma Iceland a yayin gasar. Sau hudu kenan Eagles take halartar gasar cin kofin duniya. Na farko shi ne a shekarar 1994 sai a 1998 sai a 2002 sai kuma yanzu a 2018.