✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha 2018: Gobe Najeriya za ta san matsayinta

A gobe Asabar ne idan Allah Ya kaimu za a yi wasan neman gurbi a gasar cin kofin duniya da zai gudana a Rasha a…

A gobe Asabar ne idan Allah Ya kaimu za a yi wasan neman gurbi a gasar cin kofin duniya da zai gudana a Rasha a badi.  Za a yi wasan ne a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da takwararta ta Zambiya.  Wannan shi ne wasa na biyar kuma shi ne zai tantance kungiyar da za ta haye gasar cin kofin duniya a Rasha. Wasan zai gudana ne da misalin karfe biyar na yamma agogon Najeriya a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo na Jihar Akwa-Ibom.

Najeriya dai tana fafatawa ne a rukunin B tare da kasashen Zambiya da Kamaru da kuma Aljeriya.  Kawo yanzu ita ce ke saman teburi a wannan rukuni bayan ta hada maki 10 a wasanni 4.  Sai Zambiya mai biye da maki 7 a wasanni hudu sai Kamaru mai maki 3 a wasanni 4 sai ta karshe Aljeriya mai maki daya kacal a wasanni 4.

Wasan zai yi zafi ganin cewa idan Najeriya ta samu nasara, ko shakka babu za ta cancanci zuwa gasar cin kofin duniya kenan, amma idan Zambiya ce ta samu nasara za ta hada maki daidai da Najeriya kenan watau 10-10 sai  a wasan karshe ne za a tantance kungiyar da za ta tafi gasar cin kofin duniya a Rasha.

Najeriya dai tana bukatar maki 2 ne kawai a wasanni biyun da suka rage, da hakan zai ba ta damar tafiya gasar cin kofin duniya a Rasha, hakan ce ta sa masana harkar kwallo ke ganin kungiyar Super Eagles ce za ta samu nasara ko yin kunnen doki a wasan goben amma duk da haka komai na iya faruwa.

Ana sa ran dubban magoya bayan kungiyar Super Eagles daga kowace kusurwar kasar nan ne za su hlaarci Jihar Akwa-Ibom don ganin yadda wasan zai kaya.  Fatar mu dai Allah a yi wasa lafiya, kuma a tashi lafiya.