✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rarrabuwar kai kan karba-karba ya jawo dage taron PDP

Yanzu dai an dage taron zuwa zuwa ranar Laraba da daddare

Bayan gaza samun matsaya kan batutuwan da za a tattauna a taron Majalisar Zartarwarta ta Kasa, jam’iyyar PDP ta dage taronta kan batun karba-karba har zuwa karfe 8:00 na daren Laraba.

Tun da fari dai wasu daga cikin Gwamnonin jam’iyyar sun gudanar da taron sirri a gidan Gwamnan Binuwai da ke Asokoro a Abuja.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyan mana cewa kwamitin, wanda Shugaban jam’iyyar, Dokta Iyorchia Ayu ke jagoranta, na kokarin shawo kan jagororin jam’iyar da su samar da matsaya guda da za su kai gaban majalisar zartarwarta.

Gwamnoni da sauran ’yan jam’iyar dai sun gaza amincewa kan batun da taron zai mai da hankali na karba-karbar kujerar Shugaban Kasa.

A karshe dai an dage taron jam’iyar zuwa ranar Laraba da karfe 4:00 na yamma, sai kuma na kwamitin amintattu da karfe 7:00 na yamma, yayin da na kwamitin zartarwa ya koma karfe 8:00.