Fitaccen mawakin siyasa kuma shugaban kungiyar ’yan Kannywood na 13X13, Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) ya yi hatsarin mota.
Mai magana da yawun mawakin, Rabiu Garba Gaya ne ya sanar a safiyar Juma’a cewa Rarara ya yi hatsarin ne a hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama, amma bai bayyana ko a ina ba ne.
- ’Yan ta’adda sun sace daliban Jami’ar Tarayya ta Gusau 35 a dakunan kwanansu
- Jama’ar gari sun kashe ’yan ta’adda 21 a Kebbi
A sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Facebook, hadimin a Raraya ya dora hotunan yada motar mawakin ta fada a cikin wata katuwar lambatu da kuma yadda gaban motar ya yi kaca-kaca.
Sai dai ya bayyana cewa, duk da hatsarin, Raraya yana cikin koshin lafiya.
Ga hotunan hatsarin da hadimin nasa ya fitar: