A makon nan ne, kananan yara a Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na sauran kasashen duniya wajen yin bukukuwan tunawa da ranar da ake kebe musamman don tunawa da su a kowace shekara.
A kowace shekara dai, a duk fadin duniya an ware ranar 27 ga watan Mayu don gudanar da bukukuwan ranar kananan yaran, wadanda su ne manyan gobe. Kodayake dai ababuwan da ake yi a ranar sun bambanta daga kasa zuwa kasa, sai dai dukkaninsu suna ta’allaka ne game da janyo hankali a kan muhimmanci tare da kalubalen da wannan rukunin al’umma ke fuskanta.
Muna taya yaran Najeriya murna a kan bukin ranar yaran. Ko baya ga bukukuwan, wannan rana ce da za a fito fili da irin wahalhalun da yara kanana a Najeriya ke fuskanta. A kowacce shekara dai mukan yi ta babatu cewa za mu inganta rayuwar yaran, sai dai bisa ga dukkan alamu babu wani ci gaba na a zo a gani ta wannan fuskar. Har ya zuwa yau din nan, da akwai jihohi fiye da 10 da ba su dabbaka dokar nan ta Hakkokin Kananan Yara ba. Dokar, wacce aka tsara da zimmar tabbatar da jin dadin kananan yara, an bullo da ita ne a shekarar 2003 sa’annan aka amince da ita a matsayin doka a matakin Gwamnatin Tarayya.
Kai koda a jihohin da suka sahale wa dokar, aiwatar da ita ya zama damuwa. Muhimmacin da ke tattare da dokar bai misaltuwa, sakamakon yadda ta yi tanadin yakar dabi’ar nan ta cin zarafin yara, da bautar da su ko saka su aikin wahala da auren wuri da kuma tabbatar da yancinsu na samun ilmi. Duk da irin kiraye-kirayen da wasu daidaikun jama’a da kungiyoyi da ma kafofi masu bayar da tallafi ke yi da lallai a dabbaka dokar, abin sosa rai ne matuka a ce har yanzu wasu jihohin na ci gaba da jan kafa a kan hakan, wanda ko shakka babu hakan ke sanya hakkokin yaran cikin hadari. Da yake jawabi a lokacin bikin ranar yaran a Jihar Bauchi, a bara, Babban Jami’in Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, reshen Jihar Bauchi, Mista Bhanu Pathak ya ce kin dabbaka dokar kare kananan yaran da wasu jihohin Najeriyar ke yi na shafar ayyukan da Asusun UNICEF din ke gudanarwa da ma na wasu kungiyoyin da ke da shirye-shirye a kan kananan yaran, sakamakon rashin dokokin da za su rufa wa ayyukan nasu baya.
Sai dai an c igaba da yin kunnen uwar shegu da gargadin nasa. Don haka muke kiran jihohin da har kawo yanzu ba su amince da dokar ba da su gaggauta yin hakan don ceto makomar kananan yaran tare da inganta yanayin rayuwarsu. Ko’ina a fadin duniyar nan ana bai wa kiwon lafiyar kananan yara fifikon gaske, sai dai ban da a Najeriya, inda har yanzu al’amarin kiwon lafiyar ke ci gaba da ci musu tuwo kwarya. Yayin da gwamnati ke tutiyar samar da riga-kafi da kuma kiwon lafiyar yara kasa da shekara biyar kyauta, a wasu jihohin hakan bai wadatar ba sakamakon har yanzu yaran na mutuwa a sanadin cututtukan da za a iya shawo kansu ko kuma ma riga-kafin aukuwarsu. Idan dai har muna da kudurin kare rayukan yaranmu, lallai ne a kara kaimi don tabbatar da sun sami ingantaccen tsarin kiwon lafiya.
Akwai kuma matsalar nan ta yaran da ba su zuwa makaranta. Najeriya ce dai ja-gaba ta wannan bangaren a duniya baki daya. Gwamnatoci da dama sun yi ta alkawuran rage yawan yaran da ba sa samun damar zuwa makaranta da kuma kara shigar da yaran makaranta, kash! sai dai hakan bai samu ba. Ko a makon jiya ma, sai da Ministan Ilmi Malam Adamu Adamu ta cikin jawabinsa na bankwana ya roki gafara daga ’yan Najeriya a kan rashin cika alkawarin da ya dauka na rage adadin yaran da ba sa samun damar zuwa makaranta zuwa rabi.
Ya ce, “A duk lokacin da nake halartar taruka a kasashen waje, idan aka dago batun yaran da ba sa zuwa makaranta kunya takan lullube ni. Babban abin kunya ne gare ni da kuma mu ‘yan Najeriya a matsayinmu na kasa. Najeriya ce dai ke kan gaba ta wannan fuska; koda dai ba a san mu da talauci ba. Mun yi alkawarin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta zuwa rabi. Dole ne in nemi gafara domin kuwa mun gaza ta wannan fuskar. Amma ina fatan sabon Ministan Ilmin da za a nada, ya shawo kan al’amarin.”
Muna dai ci gaba da kiran gwamnatin da ta kaddamar da shiri na gaggawa a kasa baki daya don kawar da matsalar yaran da ba sa samun damar zuwa makaranta, a cikin kankanin lokaci. Ta hanyar samar da ilmi ne kawai za mu dakile da dama daga cikin matsalolin da ke addabar zamantakewarmu da suka hada da garkuwa da jama’a da ayyukan tsageru da barace-barace da kuma auren wuri. Kamata ya yi a yi duba game da matsalolin saka yara aikin wahala da kuma safarar su, da nufin rage su ko kuma kawar da su baki daya. Batun inganta tattalin arzikin kasa ma zai matukar taimaka wa hakan, sakamakon gwadaben yara kananan da karfin tattalin arzikin iyayen nasu Danjumma ne da Danjummai.