✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar ’Yanci: Ja Rule da Ashanti za su yi gala a Najeriya

Fitattun mawakan Amurka Ja Rule da kuma Ashanti za su yi bikin gala a garin Warri da ke Jihar Delta.An shirya gudanar da bikin ne…

Fitattun mawakan Amurka Ja Rule da kuma Ashanti za su yi bikin gala a garin Warri da ke Jihar Delta.
An shirya gudanar da bikin ne a ranar 1 ga watan gobe don bikin tunawa da ranar da Najeriya ta samu ’yancin daga Turawan mulkin mallaka.
Ja Rule fitaccen mawakin gambara ne, zai barje guminsa ne tare da rakiyar fitacciyar mawakiya Ashanti a bikin da aka yi wa taken: ‘Warri Again: The Flagship’.
Cibiyar Brownhill Ebents Centre ta dauki nauyin shirya bikin galar,
Ja Rule, wanda ya fara waka a shekarar 1999 da wakar ‘Benni Betti Becci’ ya yi tashe a farko-farkon shekarun 2000 da wakokin da suka hada da ‘Betwenn Me And You’ da  ‘Always on Time’ da kuma ‘Put it On Me’.
Ashanti marubiciyar wakoki ce, kuma furodusa ce sannan jaruma, ta fara haskakawa ne da wakarta mai suna ‘Foolish’, inda makon farko da wakar ta shiga kasuwa a shekarar 2002 aka sayar da faifan wakar kwafi 503,000 a Amurka.
Manajin-Daraktar Cibiyar Brownhill Ebents Centre and Browhill Ludury billa, Misis Julie Pinnick ta ce sun kammala dukkan shirye-shirye don kayatar da ’yan kallo a bikin na bana.
Ta ce sun yanke shawarar kawo mawakan Amurka ne bayan sun fahimci hakan zai matukar kara wa bikin armashi, musamman da yake biki ne na tunawa da ranar da Najeriya ta samu ’yanci.
 “Bikin wannan shekarar ya bambanta da wadanda suka gabata, domin mun gayyato mawakan Amurka da suka hada da Ja Rule da kuma Ashanti. Mun yanke shawarar kawo mawakan Amurka ne bayan sun fahimci hakan zai matukar kara wa bikin armashi, musamman da yake biki ne na tunawa da ranar da Najeriya ta samu ’yanci.” Inji ta.