Gwamnatin Kaduna ta sanar da bude makarantu — firamare da sakandare — a fadin Jihar daga ranar Lahadi, 12 ga Satumba, 2021.
Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar a ranar Alhamis ta ce bayan bude makarantun za su koma ne a matsanyin zangon farko na shekarar karatu ta 2021/2022, — An tsallake zango na uku da ya kamata su koma.
- Yadda jama’ar gari suka kama dan bindiga da hannu a Katsina
- Buhari ya yi ganawar sirri da shugabannin kabilar Igbo
Jadawalin shekarar karatun da gwamnatin ta fitar ranar Alhamis ya nuna za a kammala zangon na farko a ranar 15 ga watan Disamba, 2021 sannan a dawo zango na biyu a ranar 9 ga Janairu, 2022.
Hakan na zuwa ne bayan sau biyu gwamnatin na dage dawowar makarantun a watan Yuli, bayan hutun suka tafi na zango na biyu.
Kwamishinan Ilimin Jihar Kaduna, Dokta Shehu Muhammad ya shaida wa wani taro a ranar Alhamis cewa, gwamnatin za ta fitar da tsarin amfani da intanet, domin cike zangon karatu na uku da aka tsallake.
Ya kuma bayyana cewa makarantun za su fara komawa a ranar da aka ayyana din ne a rukuni-rukuni.