An bayyana aladar nan ta Hausawa ta ciyayya a matsayin babbar hanyar da ke maganin yunwa da kanfar abinci a tsakanin al’umma.
Shugaban Sashen Hausa na Jamiar Yusuf Maitama Sule Dokta Yusuf Ahmad Gwarzo ne ya yi wannan bayani yayin da yake gabatar da makala mai taken ‘Al’ada madogara: Hanyoyi da mayakan magance yunwa a mahangar Bahaushe.’
Dokta Gwarzo ya ce ciyayya hanya ce mai sauki ta magance bazuwar yunwa a tsakanin alumma domin tana ba wanda bai girka abinci a gidansa ba damar ya samu ya ci abinci ba tare da ya kwana da yunwa ba.
“Idan ana yin ciyayya kowa zai samu ya ci abinci ko da kuwa ba a girka gidansa ba, babu wanda zai kwana da yunwa,” in ji shi.
- ’Yan banga sun kashe matashi da dukan kawo wuka a Zariya
- ’Yan sanda na farautar ’yan Shi’a kan Kisan ’yan sanda a Abuja
- Abin da zai hana mu biyan sabon mafi ƙarancin albashi — Inuwa
Ya kara da cewa al’adar ciyayya tana ba wa mutum damar cin abinci mai gina jiki, “duba da cewa a wannan lokacin mutum yana samun damar cin abinci iri-iri a lokaci guda.
“Ida kun duba wani zai kawo kwadon zogale wani kuma shinkafa wani kuma tuwo da sauransu.”
A cewarsa ciyayya al’ada ce da ke bunkasa zaman lafiya da daidaito a cikin alumma.
“Ta wannan hanya za a samu hadin kai a cikin alumma, kasancewar tana hada kai tsakanin mai wadata da talaka inda suke zama su ci abinci tare.
“Idan sun kammala cin abinci kuma su tattauna matsalolin rayuwa, musamman ma abin da ya shafi unguwanninsu da sauransu.”
A jawabinsa na maraba, Shugaban Kungiyar Zauren Hausa, Farfesa Garba Satatima, ya bayyana cewa an fara bikin wannan rana ne shekaru shida da sucka gabata don nuna wa duniya irin muhimmancin da harshen Hausa yake da shi da kuma kyawawan al’adu na Bahaushe.
An sanya ranar ne don dacewa da ranar da Dan Hausa ya kirkiro haruffa mai lankwasa inda Hausawa da masu kishin harshen ke taruwa da nufin bunkasa shi.
Ya ce kungiyarsu ta Zauren Hausa tana nan tana shirye-shiryen horar da malaman da ke koyar da harshen Hausa da ’yan jarida da masu tallace-talkace a kafafen watsa labarai don ganin an samu gyara ta wajen yin amfani da harshen.
Taron mai taken “Kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba,” Kungyar Zauran Hausa ce ta shirya shi, inda malaman jami’o’i da kwalejojin ilimi suka gabatar da jawabai, yayin da dalibai a nasu bangaren suka gabatar da wasannin gargajiya iri daban- daban.
Haka kuma an gudanar da gasar girkin abincin gargajiya a tsakanin daliban sakandiren jihar Kano.