✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Damokradiyya: Sakon Buhari ga ‘yan Najeriya

Yayin da Najeriya ke bukin Ranar Damokradiyya a rana mai kamar ta yau, 12 ga watan Yuni, Shugaban Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga ‘yan…

Yayin da Najeriya ke bukin Ranar Damokradiyya a rana mai kamar ta yau, 12 ga watan Yuni, Shugaban Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya.

Buahir ya ce zagayowar ranar na da muhimmanci domin tunawa da wadanda suka sadaukar da kansu wajen assasa damokradiyya da kuma bitar nasarorin Najeriya a shekaru 21 a jere na mulkin damokradiyya.

COVID-19  ta Kawo cikas

A cewarsa Najerriya na cikin mawuyacin hali musamman ga wadanda suka rasa makusantansu a annobar COVID-19 da kuma tsauraran matakan da aka dauka na hana yaduwar cutar, wadanda suka jefa mutane cikin takura.

Ya kuma jinjina wa ma’aikatan lafiya da ke aikin yakar cutar bisa sadaukar da kansu da kuma kishi da suka nuna.

Da yake bayyana tabbatar da damokradiyya a matsayin aikin gayya, Buhari ya yaba wa kusoshin siyasa da suka bayar da gudunmuwa wajen zaman Najeriya abar koyi ga sauran kasashen ta fuskar damokradiyya.

Ya ce, “A jawabina na ranar 29 ga watan Mayu na yi alkawarin magance matsalolin da ke addabarmu musamman rashin tsaro, tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa”.

Tattalin arziki:

A cewarsa a yunkurin farfado da tattalin arziki, ya mayar da hankali samar da wadataccen abinci da makamashi da albarkatun mai da ababen more rayuwa da sugabanci na gari.

Ya ce kayan da ake samarwa a cikin gida sun karu daga kashi 1.91% zuwa 2.27%, kafin bullar annobar COVID-19 da ta dagula harkokin tattalin arziki a fadin duniya.

Duk da hakan Najeriya ta kara dala biliyan 2.58 a asusun ajiyarta ta kasashen waje wanda yanzu ya kai dala biliyan 36 kuma zai isa a yi amfani da su wajen shigo da kaya na tsawon wata 7 daga kasahen wajen. Ko da yake tasirin COVID-19 a kasar ba kai sauran kasashe ba.

Harkar noma.

A bangaren noma Buhari ya ce gwamanti za ta ci gaba ba da rance domin harkar wadda ‘yan Najeriya ke kara cin rungumar matakan da aka dauka na habaka harkar noma da kuma amfani da kayan da aka noma a cikin gida.

Za kuma a ci gaba da samar da ingantaccen takin zamani mai araha, wanda yanzu akwai masana’antunsa 31 a kasar, wadanda kuma ke samar da ayyuka ga ‘yan kasa.

Sai kuma farfado da harkar noman auduga da masaku ta hanyan bayar da basuka daga bankin CBN da nunin saukaka samuwar auduga da shigo da injina daga waje, a cewarsa.

Ya kara da cewar kudaden shiga daga noman koko da ridi sun ninku daga dala miliyan 79.4 zuwa dala miliyan 153 a kokarin farfado da bangarorin da ba na mai ba.

A cewarsa an an dauki jami’ai 35,000 domin tsare albarkatun gona, yayin da ake samar da hanyoyin fitar da amfanin gona daga yankunan da ake yin noma zuwa manyan tituna.

Kasuwanci

Shugaban ya ce saukaka bayar da takardun biza da izinin kasuwanci sun taka muhimmiyar rawa a kokarin Najeriya na habaka matsakaitan masana’antu.

Buhari ya ce saukaka matakan kasuwanci ka ‘yan kasauwa daga kasashen sun daga darajar Najeriya ta zama daga cikin kasashen duniya 10 mafiya tagomashi wurin saukin kasuwanci, ta kuma kulla huldar kasuwanci da kasahsen Afirka da ma sauran duniya.

Hakar ma’adanai

A jawabinsa na Ranar Damokradaiyya,  Buhari ya ce Najeriya za ta bunkasa bangaren hakar ma’adinai.

A dalilin haka ya ba da umarnin farfado da masana’antar mulmula karafa ta Ajaokuta da hadin gwiwar gwamnati da ‘yan kasuwa.

Shugaba Buhari ya ce aiki ya yi nisa a bangaren hakar zinare, da kuma zamantar da tsarin bayar da izinin hakar ma’adanai da tara kudaden shiga a bangaren da kuma dakile zurarewan kudaden.

Inganta wutar lantarki

Ana kuma kokarin magance matsalar wutar lantarki ta hanyar gyare-gyare da fadadawa bangaren domin magance matsalar na da muhimmanci wurin raya masana’antu.

A cewarsa yarjejeniyar da Najeriya ta kulla da kamfanin Siemens zai samar tare da rarraba megawati 11,000 zuwa shekarar 2023.

Bangaren sufuri

Aikin tituna da aka gama sun hada da kilomita 412 cikin kilomita 643 da aka bayar na kudaden SUKUK, kilomita 102 a hanyar Kano-Kaduna, titin Abuja-Obajana ya kai kashi 87 da kammaluwa.

Ginin gadar Niger ta biyu ya kai kashi 48, an kuma yi kwaskwariman kilomita 4,000 na titi a fadin Najeriya.

Za a kawo karin jirage a kuma tsawaita titin jirgin Abuja-Kaduna. Za kuma tsawaita na Ajaokuta ya isa Abuja, sannan na Warri Legas su karasa tashar jiragen zuwa. Titin jirgi na Kano-Maradi da na Maiduguri-Fatakwal kuma za a cefanar.

Filayen jiragen sama kuma ana inganta zuw ana kasa da kasa da karin kayan aiki da tsare tsare.

Albarkatun mai

A bangaren mai, a karon farko cikin shekaru 10 Najeriya ta fara neman masu neman lasisin rijiyoyin mai 57 domin kara kudadaden shiga.

Akwai kuma tallafi na dala miliyan 200 domin kamfanonin mai da iskar gas na cikin gida. An kuma samu zaman lafiya da ‘ya yankin Neja-Delta.

Za a kaddamar da ofishin hukumar Neja-Delta sannan a kaddamar da ayyukan titunan yankin.

Kimiyyar sadarwa

Ma’aikatar Sadarwa da fasahar zamni ta alkinta samun layukan sadarwa da kuma yawan masu amfani da fasahar 4G.

Ilimi

Najeriya za ta ci gaba da samar da ilimi kyauta kuma dole har zuwa kammala karamar sakandare.