A ranar 17 ga watan Ramadan, aka yi Yakin Badar Tsakanin Musulmi da kafiran Makkah a zamanin Manzon Allah (SAW).
Sahabban Manzon Allah 14 ne suka yi shahada a shahararren yakin, wanda aka gwabza tsakaninsu da kafiran Makkah a wani wuri da ake kira da suna Badar a kusa da Madina.
- Abubuwan da ba a sakaci da su a Ramadan —Sheikh Daurawa
- Shekara 68 da kafa Kungiyar Dalibai Musulmi ta Najeriya
Yakin Badar wanda shi ne na farko bayan Hijirar Musulmi zuwa Madina bayan kafirai sun uzzura musu a Makka, ya wakana ne a shekara ta biyu Bayan Hijira, shekara 1,441 da suka gabata.
ِA halin yanzu an yi allon sunayen Shahidan Yakin Badar a filin da aka gwabza yakin, a wajen garin Madina a kasar Saudiyya:
Sunayen Shahidan Yakin Badar
- Umair bin Abi Wakkas
- Safwan bin Wahb
- Dhu-shamalain bn Abd Amr
- Muhji’ bn Salih
- Akil bn Albakir
- Ubaidah bn Alharith
- Sa’ad bn Khaithuma
- Mubasshir bn Abdulmundhir
- Haritha bn Suraka
- Rafi’ bn Almu’alla
- Umair bn Alhammam
- Yazid bn Alharith
- Mu’awwadh bn Alharith
- Auf bn Alharith.