✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: ’Yan sanda sun tsaurara tsaro saboda azumi a Borno

Rundunar ta ce burinta shi ne Musulmi su samu damar yin ibada cikin kwanciyar hankali.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta sanar da ƙarin matakan tsaro yayin da al’ummar Musulmi suka shiga watan azumin Ramadan.

Haka kuma, rundunar ta taya Musulmi murnar shigowar wannan wata mai alfarma.

Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa an kammala shirin tsaurara tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a cikin watan Ramadan.

“Mun san muhimmancin wannan wata ga ’yan uwanmu Musulmi,” in ji sanarwar.

“Saboda haka, mun ƙara sintiri da samar da jami’an tsaro a wurare masu muhimmanci a faɗin jihar.”

Kwamishinan ’yan sandan Borno, CP Yusufu Mohammed Lawal, ya tabbatar da cewa rundunar tana sadaukar da kai domin kare lafiyar jama’a a cikin wannan wata.

“Burinmu shi ne kowa ya samu damar gudanar da ibadarsa cikin kwanciyar hankali da tsaro,” in ji Kwamishinan.

Haka kuma, rundunar ta buƙaci jama’a da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

“Idan kun ga wani abu, ku sanar da hukuma,” in ji ASP Daso.

Rundunar ta kuma fitar da lambobin kiran kar ta kwana domin bayar da rahoto: 08068075581 da 08023473293.