✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: Tunatarwa Ga Ma’aurata

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikin sa, amin.…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikin sa, amin. Ga bayani mai kunshe da tunatarwa da nasihohi da karin bayani ga ma’aurata don su kara dagewa, da kara kaimi domin su ribaci dukkan alheran da ke cikin wannan wata na rahma na Ramadan.

Sakamako nunkin-banunki
A wani ingantaccen Hadisi, Manzon Allah ya kwadaitar da mu irin nunki-banunki na ladan da muminai suke samu a cikin wannan wata mai alfarma, inda ya ce duk wanda ya yi wani aikin nafila, to za a ba shi lada kamar ya yi aikin farilla a cikin wani lokaci da ba na Ramadan ba; kuma duk wanda ya yi aikin farilla, to za a ba shi lada kamar ya yi aikin farilla sau saba’in a wani lokaci da ba na Ramadan ba. Don haka Ramadan wata babbar dama ce gare ku ma’aurata, da za ku yi amfani da ita wajen hada kai da taimakon juna wajen ibada da karfafa imani. Idan kuka hada kanku wajen yin bautar Allah (SWT), tare da taimakon juna wajen karfafa imani da inganta ibada, ko shakka babu wannan zai kara karfin so da kaunar da ke tsakaninku, wacce ake sa ran in sha Allah ita ma Allah zai nunka maku sakamakonta, da fatan Allah ya sa mu dace da dukkannin alheran da ke cikin wannan wata, amin.
Dagewa da addu’a:
Ya ‘yan uwana ma’aurata! Mu sani fa wannan wata ne na amsar addu’a da karbar tuba, dukkanmu muna da dimbim bukatun da ba za su kirgu ba, kuma dukkaninmu masu laifuka ne da ba mu san iyakarsu ba, don haka kada mu yi sanya.Yana da matukar alfanu gare mu da mu zauna mu rubuta dukkan bukatunmu gaba daya a takarda, ya kasance idan mun zo yin addu’a sai mu dauko mu karanta su ta haka ba za mu mance da ko daya ba daga cikin bukatunmu. Da fatan Allah ya amsa mana addu’o’inmu da dukkansu, kuma ya sa mu dace da dukkan alherai da albarkar wannan wata na Ramadan, amin.
Yin hakuri da iyali:
Musamman yara, sai a daure kar a rika yi masu tsawa ko yi masu fada cikin fushi. A yi masu magana cikin hakuri da lallashi. Manzon Allah Sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Idan dayanku na azumi, sai ya guji yin mummunar magana da kace-nace; in kuma wani ya neme shi da fada, sai ya ce da shi ni ina azumi.”
daukar darussan daga cikin watan Ramadan:
Ma’aurata su dauki wannan watan kamar wani lokaci ne na yin kos don karfafa zumuntar aurensu, da kuma karfafa imaninsu. Akwai darussa masu matukar alfanu da ma’aurata za su koya a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan; muhimmai daga cikinsu akwai:
Hakuri; kamar yadda ma’aurata suke hakurin dawainiyar da ke tattare da daukar azumi, to haka ma sai su koyi yin hakuri da junansu.
Kyautatawa: Sai ma’aurata su yi dubi ga irin ni’imomi da alheran da Allah Madaukakin Sarki ya saukar mana a wannan wata mai alfarma, hakan sai ya koyar da su, su kara kaimi wajen kyautatawa da jiyar da juna dadi.
Kau da kai ga kasawar juna: Wannan watane da Allah yake yin gafara a cikinsa, yake kuma ‘yanta wasunmu daga shiga wuta, duk kuwa da irin dimbin sabon Allah da butulce wa dokokinsa da muke yi. Sai ma’aurata su yi koyi da wannan darasi wajen amince wa juna, gafarta wa juna, da kaunar junansu duk da rauni, kasawa ko wani laifin da ya gabata na zaman tare a rayuwarsu.
Danne fushi: Azumi na ladabtar da zuciya da gangan jikin dan Adam ta fannin bukatunsu na yau da kullum. Kamar yadda ma’aurata suka iya danne yunwa da kwadayi da bukatunsu a cikin wannan wata, sai su yi koyi da wannan darasi wajen danne fushin da bacin ransu, kar su bari ya bayyana balle har ya haifar da wani kulli maras dadi a cikin dangantakarsu.
Yin kiyamullayli tare da yara duka:
Ummuna Aisha(R.A)ta ce idan goman karshe na Ramadan ya zo, Annabi (SAW) yana raya dare gaba dayansa, sannan zai tayar da iyalansa su ma don su raya dare. Don haka sai ma’aurata su dage wajen yin koyi da wannan kyakkyawar sunnah ta Annabinmu (SAW); sai a riki dabi’arsa yara su yi barci da wuri don tashi tsakar dare ya yi masu sauki sosai. Kuma maigida na iya sa wata ‘yar kyauta ga duk wanda ya dage daga cikin yaransa wajen yin kiyamullaili da karatun al-kur’ani don hakan zai sa su kara dagewa sosai. Da fatan Allah ya yi mana gam-da-katar mu zama daga cikin wadanda za su raya dukkan dararen watan Ramadana da kyawawan ibadu, amin.
Kyauta da kyautatawa ga miskinai da makwabta:
Sai ma”aurata su yi koyi da Manzon Allah (SAW) yadda yake kara yawan kyauta a cikin wannan wata mai alfarma; za su iya yin haka ta wadannan hanyoyin:
Hada kayan buda baki na alfarma da aikawa da su ga wadanda aka san ba su da halin irinsa.
Gayyatar marasa galihu zuwa walimar buda baki.
Kyautar kayan Sallah ga mabukata daga ‘yan uwa, makwabta da sauran miskinai da sauran makamantan kyawawan aiyuka.
Tsiro da wani kyakkyawan aiki da kuma dagewa da aikata shi har sai ya zama dabi’a. Kamar yawan murmushi, yawan sada zumunci; saukaka mu’amala ga jama’a. Yawan sadaka da taimakon marasa galihu; kyautata zatto ga jama’a, yawan yin addu’a ga ‘yan uwa Musulmi; dagewa wajen neman ilmi, musamman na kadaita Allah wajen bauta da kuma na yin bautar, yin Salatul duha; da yawaita tuba ga Allah daga wani sabo da aka aikata, kuma daga baya aka yi nadamarsa da sauransu.
Da fatan Allah ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.