✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: Muhimman bayanai ga mata

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Da fatan kuna cikin koshin lafiya. Sakamakon shigowar watan ramadana sai na ga dacewar in yi…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Da fatan kuna cikin koshin lafiya. Sakamakon shigowar watan ramadana sai na ga dacewar in yi tunatarwa kan fa’ida da kuma falalar da ke cikin watan.
Sau da dama mata kan fake da cewa aikin gida wadanda suka hada da shirya abincin buda baki ko suhur da sauransu ke hana su aikata ayyukan ibada, wanda za ka samu daga an sha ruwa sai su rika ji tamkar an yi musu dukan kawo wuka, a lokaci guda suka kasa katabus. A gaskiya wani lokacin sakacin mata ne yake janyo hakan, abin da nake nufi da hakan shi ne, ba sa tsara yadda za su gudanar da ayyukansu, sai ka samu sai lokaci ya kure kafin su fara gudanar da ayyukansu, wanda hakan kan sanya su rika yin aikin cikin sauri, daga zarar sun kammala kuma, sai su yi laushi kamar hatsin da aka nika.
Idan har kuna so ku samu damar gabatar da ibadu a watan ramadana ya kamata ku rika fara gudanar da ayyukan gida da wuri.
A wannan rubutun zan kawo wadansu abubuwa masu fa’ida da falala da kuma muhimmanci da ya kamata ku rika yi a lokacin azumi da ma bayansa. Ina fata za ku bi bayanin sau da kafa don yin gam da katar da fa’idojin bayanin.
Azumi shi ne, ku kame daga cin abinci da shan abin sha da jima’i (idan kuna da aure) da sauran abubuwan da za su iya karya muku azumi, tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin da’a da biyayya ga Allah (SWT). Ubangiji Ya ce: “….Ku ci, ku sha har silili fari ya bayyana a gare ku daga silili baki daga alfijir, sannan kuma ku cika azumi zuwa ga dare…”
Akwai bukatar mai yin azumi ya rika yin suhur. Sau da dama wadansu matan kan girka abincin suhur, amma sai su ki ci, inda sai ka ga sun koma barci abinsu ba tare da yin suhur din ba. Masu yin hakan da sun san falalar da take ga yin suhur da ba za su yi sake su dauki azumi ba tare sun yi suhur ba.
Yana da matukar fa’ida ga wanda zai yi azumi ya yi suhur, amma babu wani abu idan mai azumin ya bar suhur ba tare da ya yi ba. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku yi suhur, domin suhur albarka ne ga masu azumi.” Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. Don haka ya kamata ku dage wajen yin suhur.
Jama’a da dama ba su san daga wani lokaci ne ake fara yin suhur da kuma lokacin da ake tsaya ba, ganin hakan ne ya sanya zan fito da abin fili don a fahimce shi sosai. Za a iya fara cin abincin suhur daga tsakar dare zuwa lokacin da alfijir zai keto. Zaidu Ibn Thabit ya ce: “Mukan ci abincin suhur da Manzon Allah (SAW), kafin mu shiga sallar Asuba. Da aka tambayi shi lokacin da ke tsakanin yin suhur da kuma shiga sallah, sai ya ce: “Lokacin da za iya karanta matsakaitan ayoyi hamsin.” Bukhari da Muslim sun rawaito shi.
Bayan bayani a kan suhur sai lokacin da za a yi buda baki. Ana bukatar idan kun yi azumi, sai ku hanzarta yin buda baki daga zarar rana ta fadi. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Yana da kyau idan har mutane suka yi azumi, to su gaggauta yin buda baki.” Bukhari da Muslim suka rawaito shi.
Akwai wani abu da yawancin mata suka manta da shi, inda suka dauka sai dai maza ne suke yi, wato goge baki da aswaki. Ana so mai azumi (namiji ko mace) ya rika goge bakinsa da aswaki yayin da yake azumi. Saboda Manzon Allah ya ce a yi amfani da aswaki yayin da ake azumi. Haka mutum zai iya amfani da man goge baki matukar ba zai hadiye shi ba.
Sau da dama mata kan tsaya kallace-kallace, inda suke cewa yin hakan yana sanya lokaci ya wuce ba tare da sun sha wahalar azumi ba. Maimakon kallon da za ku yi ya kamata ku yi karatun Alkur’ani ne, ko ku rika sauraren tafsirai, ku yawaita zikiri da hailala da istigfari.
Ko ba a lokacin azumi ba akwai fa’ida da lada masu yawa ga mutumin da yake karanta Alkur’ani, sai dai an fi samun fa’ida da kuma lada marar adadi idan aka aikata hakan a lokacin watan Ramadana.
Bukhari ya karbo daga Ibn Abbas, inda yake cewa: “Manzon Allah shi ne mafi fifikon kyautatawa, ya kuma fi aikata hakan musamman a lokacin Ramadan. Yana kuma koya mini karatun Alkur’ani…”
A karshe ina fata za ku yi amfani da bayanan da na kawo muku a matsayin wata matakala da za ta kara hawar da azuminku zuwa ga kaloluwar samun matsayi. Allah Ya taimake mu, amin.