Tsohon Sakataren Riko na Jam’iyyar APC na Kasa, Tijjani Tumsah, ya yi kira ga al’ummar Musulmi su yi amfani da watan Ramadan wurin yin addu’o’in kawo karshen matsalar rashin tsaro da ta addabi Najeriya.
Ya kuma bukaci Musulmin Najeriya da su daga da addu’o’i don ganin an kawo karshen cutar COVID-19.
- Ramadana: Tsohon Gwamna ya raba kayan abinci na Naira biliyan 1.4 a Zamfara
- ‘Dalilin da muke so Gwamnan Bauchi ya yi takarar Shugaban Kasa’
A cewarsa, wajibi ne Musulmi su zama cikin shiri kan abubuwan da suke faruwa a fadin duniya na tabarbarewar sha’anin tsaro, don haka ya bukace su da su kai rahoton duk wani abu da ba su gane masa ba ga jami’an tsaro
Tumsah, ya bukaci daukacin ’yan Najeriya da su roka wa Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari lafiya da fatan ya dawo gida lafiya daga ganin Likita da ya je asar Ingila.
A karshe, ya yi kira ga daukacin Musulmi da su rubanya ayyukansu na alheri a wannan wata mai alfarma.