Kungiyar cigaban Matasan Yobe (YOYICOD) ta tallafa wa magidanta ’yan gudun hijira da marasa galihu 25 a garin Gashua da ke Karamar Hukumar Bade a Jihar don rage musu radadin kuncin rayuwa saboda falalar ciyarwa a watan azumi.
Shugaban YOYICOD, Ibrahim Sunusi, yace sun raba tallafin ne da nufin taimaka wa marasa galihu, ta hannun Isiyaku Hamisu Dan Gatan Sidi Bash da hadin gwiwar Zawiyatul Malam Garba Mai Tafsiri.
Ya ce kungiyar ta bi gida-gida domin raba wa magidantan tallafin a matsayin somin-tabi.
A cewarsa shirin nasu na gaba zai fi haka, domin a halin yanzun abun ya zo ne ba tare da wani kwakkwaran shiri ba.
Ibrahim Sunusi, ya ce kofarsu a bude take ga duk mai hannu da shuni ko kungiya da za su hada kai wajen fadada shirin, domin taimaka wa gajiyayyu da marasa galihu.
Daga karshe, ya jinjinawa gwamnatin Jihar Yobe, bisa yadda take taimaka wa ’yan gudun hijira da marasa galihu a Jihar, don ganin sun dogara da kansu.