✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: Lokuta 5 da ya kamata a ribace su

Lokutan da ayyukan alheri ke da matukar muhimmanci a cikinsu

A yayin da al’ummar Musulmi suka shiga kwana 10 na biyu a watan Ramadan na 1443 bayan Hijira, sai kara jajircewa suke yi domin samun rabauta da alheran da ke cikin watan mai alfarma.

Ga wasu muhimman lokuta biyar da ya kamata kada a yi sakaci da su, musamman a wannan wata kamar haka:

1- Lokacin sahur

Sahur yana kasancewa ne kafin fitowar Alfijir na biyu, tun daga sulusi na uku na karshen dare. 

Wannan lokaci, wato kashi daya cikin uku na karshe a cikin dare, yana daga cikin lokutan da ake amsa addu’a.

Manzon Allah (SAW) ya ce, idan sulusin karshe na dare ya yi, Allah Madaukakin Sarki Yakan saukowa sama ta daya, saukowar da ta dace da Shi, Ya rika cewa, “Shin akwai wani mai neman yafiya in gafarta masa? Ina mai rokon wani abu, in biya mishi bukata?”

Saboda haka sai a dage da yin ibada da kuma addu’o’in neman samun Aljanna da alheran duniya da lahira, tare da neman kariya daga wuta da kuma dukkan sharrin duniya da lahira a wannan lokaci.

2- Alfijir da La’asar

A lokacin fitowar Alfijir na biyu da kuma lokacin La’asar ne mala’iku masu rubuta ayyukan bayi suke yin canjin aiki.

A kullum, da yamma mala’ikun da ke rubuta ayyukan bayi daga fitowar Alfijiar zuwa yamma ke canzar masu rubuta ayyuka daga yamma zuwa wannan lokaci.

Idan mala’ikun da suka mika aiki suka koma, Allah zai tambaye su, alhali Shi ne mafi cikakken sani, game da abin da suka je suka samu kowane bawa yana aikatawa.

Haka kuma yana tambayar su abin da bawan yake aikatawa a lokacin da suka baro shi.

Saboda haka, domin samun kyakkyawan shaida daga wurin mal’aiku a gaban Allah, yana da kyau mu dage wajen yawaita ambaton Allah da kuma sauran ayyukan ibada a wadannan lokuta masu muhimmanci.

3- Bayan sallar farilla

Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda ya yi sallar farilla sannan ya zauna ya ci gaba da ambaton Allah, mala’iku za su yi ta roka mishi gafara da rahama a wurin Allah.

4- Sallar Asuba zuwa fitowar rana

Shi ma lokaci ne mai matukar muhimmanci da kuma albarka.

Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda ya yi Sallah Asuba, sannan ya zauna ya ci gaba da ambaton Allah har rana ta fito, sannan ya yi sallar nafila raka’a biyu, za a ba shi ladar aikin Hajji cikakke.

5 – Bayan kiran sallah

Kamar yadda muke burin samun rahamar Allah da kuma ceton Manzon Allah (SAW), ya kamata mu ribaci lokacin da ladan ya kammala kiran sallah.

Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) cewa duk mutumin da ya amsa kiran sallah, bayan na kammala kuma ya yi salatin Annabi da zikirin (Allahumma rabba hazihid da’awatit taam maati was salatil ka’ima, har zuwa karshe) zai samu ceton Manzon Allah a ranar Lahira.

Allah Ya sa mu dace.