Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta sanar da haramta wasan tashe a watan Ramadan a kwaryar birnin Kano.
A bisa al’ada, a kan fara wasan tashe ne daga 10 ga watan azumin har zuwa karshensa, inda mutane kan yi wasa iri-iri yayain da mutane kuma ke ba su kyaututtuka.
- Wadanda suka sace mutum 100 a Zamfara na neman miliyan 60 a matsayin kudin fansa
- Lampard ya fara da kafar hagu bayan dawowa Chelsea
To sai dai a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta bakin Kakakinta, Abdullahi Haruna Kiyawa, ta ce an haramta al’adar ce a bana, kamar bara ma, saboda fargabar samun rikici.
Ya ce sun dauki matakin ne saboda yadda bata-gari ke fakewa da dadaddiyar al’adar wajen aikata laifuka irin su daba kwacen waya, shaye-shaye da sauransu
Ya sha alwashin jami’ansu za su kama duk wanda aka samu ya yi kunnen uwar shegu da dokar.
Kazalika, rundunar ta ce har yanzu haramcin da ta sanya a kan yin kilisar dawakai ba bisa ka’ida da kuma yin wasan tartsatsin wuta ko fasa naka-awut lokacin bukukuwa na nan daram.