✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: An rage wa ma’aikata lokacin aiki a Jigawa

Ana sa ran ma’aikatan su ribaci lokacin su yi wa jihar addu’ar samun habakar tattalin arziki.

Gwamnatin Jigawa ta rage wa ma’aikatan jihar lokacin aiki na awanni 2 albarkacin watan azumin Ramadana na wannan shekara ta 2023.

Mai magana da yawun ofishin Shugaban Ma’aikata na jihar ta Jigawa, Ismail Dutse ne ya bayyana hakan a birnin Dutse a sanarwar da aka raba wa manema labarai.

A cewar Alhaji Isma’ila Ibrahim, a halin yanzu ma’aikatan jihar za su je wuraren aiki ne da misalin karfe 9 na safiya su kuma tashi da misalin karfe 3 na yamma a tsakanin ranakun Litinin zuwa Alhamis maimakon su je wuraren ayyukan su da misalin karfe 8 su kuma tashi karfe 5 na yamma.

Mai Magana da yawun Ofishin Shugaban Ma’aikatan ya kuma yi bayanin cewar, makasudin daukar wannan mataki shi ne, bai wa ma’aikatan jihar damar bauta wa Allah a yayin azumi da kuma yin bude baki a kan lokaci.

Haka kuma ya ce hakan zai bai wa ma’aikatan damar yi wa jihar addu’ar samun zaman lafiya da habakar tattalin arziki.

Sai dai sanarwar ta ruwaito Shugaban Ma’aikatan Jihar, Hussaini Kila, za a ci gaba da aiki a ranakun Juma’a daga karfe 9:00 zuwa 1:00 kamar yadda aka saba.