✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Raliya Ta Dadinkowa Za Ta Shige Daga Ciki

A yammacin ranar Alhamis manyan jaruman Kannywood za su halarci liyafar daurin auren Raliya ta shirin Dadinkowa

Za a daura auren Amina Mu’azu Lawan wacce aka fi sani da Raliya a cikin shirin Dadinkowa a ranar Juma’a.

A yammacin ranar Alhamis manyan jaruman masana’atar Kannywood za su halarci liyafar daurin auren Raliya ta shirin Dadinkowa, wadda nan da sa’a 24 masu zuwa za ta shige daga ciki.

A ranar Juma’a 22 ga watan Yuli, 2022 za a shafa Fatihar auren Raliya mai fitowa a cikin Dadinkowa, wasan kwaikwayo mai dogon zango na tashar talbijin ta Arewa24 za ta zama amarsu ta ango.

Aminiya ta samu labarin za a daura auren ne Masallacin Juma’a na tsohuwar harabar Jami’a Bayero ta Kano bayan an idar da Sallar Juma’a.

Ana sa ran manya-manyan jaruman Kannywood ciki har da masu fitowa a shirin Dadinkowa da kuma Kwana Casa’in na tashar Arewa24 za su halarci walimar ta ranar Alhamis.

Dadinkowa shi ne wasan kwaikwayo da Raliya ta fara fitowa a matsayin jaruma, a inda ta samu karbuwa ita da kannenta, Rufa’i Yakubu, wanda ke fitowa a shrin a matsayin Salihi.

Bugu da kari, mahaifiyarta ta dade a hakar fina-finan Hausa, inda take fitowa a cikin shirin na Dadinkowa a matsayin Sabuwa, matar Ayuba Maigadi.

%d bloggers like this: