✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rahoton Sahara Reporters ya fusata dubban Musulmi

Dubban musulmai sun shiga Allah wadai tare da tsine wa Sahara Reporters.

Wani rahoto da jaridar nan ta Sahara Reporters mai buga labarai ta yanar gizo ta wallafa, ya janyo tofin Allah-tsine da fusata dubban Musulmi.

Musulmi da kungiyoyi da dama a ranar Litinin sun yi tir da kungiyar Afenefire da kuma jaridar kan rahoton wanda suke zargi da batanci ne ga Manzon Tsira, Annabi Muhammad (SAW).

  1. ’Yan IPOB sun kashe DPO a mahaifar Gwamnan Imo
  2. Firai Minista mace ta farko a Samoa ta hau mulki

Kungiyar Yarabawa da Zamantakewar Al’adu ta Afenifere, ta ce ba ta ga wani aibu ba don Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya nemi ballewa da nufin kafa wata kasar.

Sakataren Kungiyar na kasa, Jare Ajayi, ya kwatanta tserewar da Igboho ya yi zuwa Jamhuriyar Benin tamkar Hijirar da Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W) ya yi daga Makkah zuwa Madinah.

Sai dai wannan furuci ya tayar da kura matuka, inda Musulmi da kungiyoyi suka shiga tsine wa jaridar da kuma kungiyar.

Wadanda suke tofin Allah-tsine sun dauki lamarin a matsayin kalaman batanci ga Manzon Allah Tsira da Amincin Allah Su kara tabbata a gare shi.

Tuni aka fara gangamin toshe shafin Sahara Reporters da ke kafafen sada zumunta tare da kokarin daukar matakin shari’a a kansu.

Hadimin Shugaban Kasa na musamman kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya rubuta cewa, “Kalaman da Afenifere ta yi na kwatanta Annabinmu, abin kauna (S.A.W) da Sunday Igboho da Sahara Reporters ta ruwaito abin Allah wadai ne.

“Su biyun ba za su taba kwatantuwa ta kowace hanya ba.

“Ina matukar nuna rashin amincewa tare da yin Allah wadai da wannan kalamai sannan ina neman dukkan Musulmi da su la’anci tare da kai karar Sahara Reporters,” a cewar Bashir Ahmad.

Dubun dubatar Musulmi sun shiga kai karar shafin Sahara Reporters tare da neman a rufe shi baki daya, inda suka rika amfani da hoto mai dauke da sakon nuna rashin goyon baya ga jaridar.

Hoton nuna rashin goyon baya ga Jaridar Sahara Reporters da wadanda suka fusata suka rika amfani da shi.

Sai dai bayan yunkurin kai karar Sahara Reporters da bayyana fushi da dubban mutane suka yi, jaridar ta cire rahoton da ya yamutsa hazo.