Mabambantan ra’ayoyi sun biyo bayan fitar da rahoton da masu sanya ido kan zabe na Kungiyar Tarayyar Turai suka gabatar game da zabubbukan da suka gabata a bana da suka hada da zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa wadanda aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairu da kuma zaben gwamnoni da na ’yan Majalisar Jihohi da aka yi a ranar 2 ga watan Mayu. An gabatar wa Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Farfesa Mahmoud Yakubu rahoton ne ta hannun ’yar Majalisar Dokoki ta Kungiyar kuma daya daga cikin jami’an da suka sa ido a kan yadda zabubbukan suka gudana, Maria Arena.
Tarayyar Turan ta aiko da jimillar masu sa ido 91 a zaben Shugaban Kasa kuma ta turo da 73 a zabubbukan gwamnoni daga bisani kuma ta turo da masu sa ido 20 don su duba zabubbukan cike-gurbi da aka gudanar. Rahoton dai wata manuniya ce ga irin ci gaba da kuma koma bayan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta samu a ayyukanta. Sannan yana kunshe da wasu hanyoyi 30 da za su iya taimakawa wajen kawo ingancin ayyukan wannan hukuma. A cikinsu akwai lurar da suka yi da wasu tangardodi da ke tattare da yadda ake gudanar da zabe wadanda suka nuna raunin hukumar da kuma matsalar rashin fitowa zabe da jama’a suka yi a zabubbukan.
Wasu muhimman abubuwa da masu sa idon na Tarayyar Turai suka yi tsokaci a cikin rahoton nasu akwai yadda Hukumar INEC ba ta iya gabatar da matattarar bayanai ta bayanan na’urorin tantance katunan zabe ba wajen tattara sakamakon zabe. Rahoton ya yi kira ga Hukumar INEC da ta inganta hanyoyin tattara sakamakon zabe saboda kara Wa masu zabe Kwarin gwiwa a kan sakamakon zaben da hukumar ke bayyanawa. Wani muhimmin batu kuma da suka yi tsokaci a kansa shi ne cewa kotuna ya kamata su rika gaggauta yin shari’un rikicin zaben cikin gida da suke gabansu kafin zabe don gudun kada a rika maimaita wasu shari’u a gaban kotuna daban-daban wadanda kuma hakan yana iya jawo tsaiko ko ya kawo karan-tsaye ga shirye-shiryen zabe.
Rahoton na masu sa ido na Tarayyar Turai ya ja hankali daga bangarori da dama. Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya yaba wa wannan rahoto tare da yin alkawarin aiwatar da shawarwarin da suka ba da a nan gaba. A nasu bangaren Kungiyar Tarayyar Turan ta jinjina wa Hukumar zaben ganin yadda ta aiwatar da wasu daga cikin shawarwarin da kungiyar ta gabatar mata a zaben shekarar 2015 da ya gabata. Da yake tsokaci a kan wannan rahoto Mataimakin dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP Mista Peter Obi cewa ya yi rahoton ya fito da duk wata badakala da take tattare da yadda ake gudanar da zabubbuka a Najeriya. Shi kuwa Mai magana da yawon jam’iyya mai mulki wato APC Festus Keyamo cewa ya yi rahoton bai kammala ba don ya yi waskiya.
Kunshiyar rahoton na masu sa idon dai ya bayyana cewa zaben da aka gudanar a bana bai kai bantensa ba. Masu sa idon dai sun kasance a cikin kasar nan na tsawon watanni suna sanya idanu a kan matakan da ake bi don kaiwa ga gudanar da zabubbukan ciki har da yadda ake gudanar da tarurruka da ’yan jaridu da yadda jam’iyyu suke gudanar da kamfe da kuma yadda kotuna suka rungumi wasu daga cikin kararrakin da suka shafi zabe da suke a gabansu. Ga misali a cikin rahoton sun caccaki yadda Shugaban Kasa ya kori Babban Joji Najeriya inda suka ce hakan ya saba wa ka’ida.
Mafiya yawan tangardodin da suka gabatar dai masu sanya ido akan zabe na cikin gida da kuma kafafen watsa labarai sun gabatar da su ga hukumar tun farko. Akwai yawan tashe-tashen hankula da aka samu a Jihar Ribas wadannda suka salwantar da rayukan mutane da yawa wanda kuma ya yadu zuwa wasu sassa na kasar nan yana daga cikin abubuwan da suka zayyana. Haka shigar jami’an tsaro dumu-dumu cikin harkokin zabe a wasu yankuna na kasar nan kamar yadda ita kanta Hukumar INEC ta yi tir da zargin shigar masu kakin soja cikin harkar zabe a Jihar Ribas shi ma ya dauki hankali. Majalisar Wakilai ta kafa wani kwamiti wanda ta dora maSA alhakin binciken zargin da ake yi na shiga harkar zabe da jami’an soja suka yi a Jihar Ribas. Haka jami’an sa-idon sun yi tir da yadda Shugaba Buhari ya ki sanya wa dokar zabe da aka gyara hannu duk da yake ’yan majalisa sun riga sun kammala aikinta. Don haka suka ce ya kamata a gaggauta sanya mata hannu tunda zabubbuka sun wuce.
Don haka muna kira da babbar murya ga Hukumar INEC ta sanya idon basira ta kalli wadannan shawarwari da Tarayyar Turai ta gabatar mata tare da aiwatar da su kafin zuwan zabe na gaba. Haka kuma ya zama wajibi hukumar ta dubi shawrwarin da Kungiyar Tarayyar Afirka da kuma Kungiyar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma suka gabatar mata don inganta harkokin zaben a nan gaba.