✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rahama Sadau za ta gana da ‘gwanarta’ Priyanka Chopra

Fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood Rahama Sadau ta kusa ganawa da gwanarta Priyanka Chopra ta Indiya. Saboda tsananin kaunar da Rahama ke yi wa Priyanka ya…

Fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood Rahama Sadau ta kusa ganawa da gwanarta Priyanka Chopra ta Indiya.

Saboda tsananin kaunar da Rahama ke yi wa Priyanka ya sa ha rake kiran ta suna Rahama Priyanka.

ita dai fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Indiya na Bollywood wato Priyanka Chopra ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta ce tana fatan haduwa da Rahama Sadau wani dan lokaci kadan mai zuwa.

Tun farko dai, Jaruma Rahama Sadau ce ta aika da sakonta zuwa ga Priyanka Chopra ta hanyar wallafawa a shafin Priyanka na Twitter inda ta nuna mata irin burin da take da shi na kasancewa kamar ta, inda ta ce “Idan na duba irin nasarorin da kika cimma, ina kara samun karfin gwiwa na zama kamarki” –  Kamar yadda Rahama Sadau ta aike wa Priyanka Chopra.

Jim kadan bayan aike wad a wannan sakon sai Rahama ta samu amsar kalmominta daga Priyanka Chopra wadda ta amsa mata da cewa: “Ina godiya a gare ki Rahama Sadau. Ina Fatan haduwa da ke nan ba dadewa ba. Ina kaunarki kuma ina fatan alheri a gare ki a dukkan komai” – Inji Jaruma Priyanka Chopra.

Jaruma Sadau ta nuna murnarta matuka ganin yadda ta samu wannan amsar cikin sauri da kuma kalamai masu dadi, sannan ta ayyana cewa tana nan tana jiran lokaci.

Rahama Sadau dai tad ade tana kaunar Priyanka Chopra, inda saboda tsaninin kaunar tad a take yi yasa ake mata lakabi da Priyanka a masana’antar shirya finanan Kannywood. Sannan kuma duk wanda ya santa, ya san bat a boye kaunar da take yi wa Priyanka. Yanzu za a iya cewa nesa ta zo kusa ga Rahama Sadau.