✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rahama Sadau ta sadaukar da kudin da ta tara a sabon fim dinta ga masu karamin karfi

Za ta bayar da kudin ne ta hannun gidauniyar da ta kafa mai suna Ray of Hope.

Fitacciyar jarumar fina-finan nan a masana’antar Kannywood, Rahama Sadau, ta ce ta sadaukar da dukkan kudin da ta samu a sabon fim dinta mai suna Nadeeya don tallafa wa masu karamin karfi.

Za ta bayar da kudin ne ta hannun gidauniyar da ta kafa mai suna Ray of Hope.

Jarumar ta sanar da hakan ne a wata tattaunawarta da gidan talabijin na Liberty ranar Litinin.

A cewarta, za a yi amfani da kudaden ne wajen ayyuka da shirye-shirye daban-daban da gidauniyar tata ke yi wajen tallafa wa marasa karfi, ciki kuwa har da almajirai.

Kazalika, ita ma gidauniyar ta Ray of Hope ta tabbatar da tagomashin, inda ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, “[Rahama Sadau] Ta sadaukar da duk kudaden da sabon fim dinta mai suna Nadeeya ya tara ga wannan muhimmiyar gidauniyar.

“Muna matukar godiya da yabawa kan wannan abin alherin. Za mu tabbatar an yi amfani da dukkan kudaden yadda ya dace. Muna godiya sarauniya Rahama Sadau”.

Labarin dai ya jawo yabo da san-barka daga mutane da dama, musamman a shafukan sada zumunta.

Jaruman masana’antar Kannywood da dama ne suka halarci wajen kallon fim din da aka fara haskawa a makon da ya gabata a sinimar da ke rukunin shagunan Ado Bayero Mall da ke Kano.

Rahama Sadau dai, wacce jaruma ce da ke fitowa a fina-finan Hausa da na Kudancin Najeriya (Nollywood), a kwanan nan kuma ta fara fito wa a fina-finan Indiya.