Gamayyar kungiyoyin ’yan kwadago a jihar Kano sun bai wa gwamnatin jihar wa’adin makonni biyu ta janye batun zaftare albashin ma’aikatan jihar da ta yi ko kuma su tsunduma yajin aiki.
Shugaban Kungiyar ‘Yan Kwadago ta Kasa reshen jihar, Kwamared Kabiru Ado Minjibir shi ne ya bayyana hakan yayin wanin taron manema labarai da kungiyoyin suka kira a Kano ranar Laraba.
Ya ce kungiyoyin za su tsunduma yajin aikin ne na tsawon kawanaki bakwai matukar aka gaza biya musu bukatunsu, yana mai nuni da cewa ragin ya zo musu da ba zata kuma ya sabawa ka’ida.
A cewarsa, wa’adin da kungiyoyin da yawansu ya kai 13 su ka bayar zai fara aiki ne daga ranar Laraba, 27 ga watan Mayun da mu ke ciki kafin daga bisa su tsunduma yajin aiki na tsawon kwanaki bakwai.
Minjibir ya kara da cewa ragin ya sabawa tanade-tanaden Dokar Kwadago ta Kasa ta 1974 da kuma wasu yarjeniyoyi na kasashen duniya daban-daban da Najeriya ta sanya wa hannu.
Ya ce kungiyoyin sun yanke shawarar yin fatali da abinda suka kira ragin da ba yak an ka’ida, su na masu kira ga gwamnatin da ta mutunta dokar mafi karancin albashi tare da kiyaye kara zaftare musu albashin a nan gaba.
“Gwamantin Kano ta saba yarjejeniyar mafi karancin albashi na 2019 wadda gwamnati da ‘yan kwadago suka cimma, ‘yan majalisu su ka mayar doka kuma shugaban kasa ya rattaba wa hannu”, in ji shugaban ‘yan kwadagon.
Ya kara da cewa, “Hakazalika, gwamnatin ta gaza aiwatar da biya kudaden ariyas ga ma’aikatan kananan hukumomi, ma’aikatan lafiya a matakin farko, malaman firamare da sakandire, malaman manyan makarantu da ma’aikatan bangaren lafiya.
“Hakan ya sa gwamnati ta yi wa ma’aikatan ‘yar burun-burun wajen aiwatar da biyan hakkokin ba tare da sanin kungiyoyin mu ba.
“Kamata yayi ma’aikata masu ayyuka da suke cikin barazana sakamakon mu’amala da masu dauke da cutar Korona kamar ma’aikatan lafiya da ‘yan jaridu su sami wata kulawa ta musamman ta hanyar biyansu kudaden alawus, kuma su rika cin gajiyar inshorar lafiya kamar yadda dokar gwamnatin taryya ta yi tanadi.
Bugu da kari, kungiyoyin kwadagon sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta biya kudaden ariyas da duk wani nau’i na ma’aikatan gwamnati ke bin jihar daga watan Aprilu zuwa Nuwambar bara.
Aminiya ta rawaito yadda a makon da ya gabata ma’aikata a jihar Kano suka koka kan yadda aka zaftare albashinsu na watan Mayu ba tare da wani cikakken bayani ba.
Matakin kuma ya biyo bayan sanarwar da gwamnatin jihar ta yin a rage albashin duk masu rike da mukaman siyasa sakamakon raguwar kudaden shigar da ta ke samu a cikin gida da kuma gwamnatin tarayya.