✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rabon nama

Zaki da kura da dila suka tafi farauta, suka kashe batsiya da barewa da zomo. Zaki ya ce: “Kura tashi ki raba mana.” Kura ta…

Zaki da kura da dila suka tafi farauta, suka kashe batsiya da barewa da zomo. Zaki ya ce: “Kura tashi ki raba mana.” Kura ta ce: “Har da wani rabo ne? Kai ka dauki batsiya, dila ya dauki zomo, ni in dauki barewa.” Ashe zaki bai so wannan rabo ba, ya zabura ya buge kura, kanta ya rabe biyu. Ya ce: “Malamin dawa, zo ka raba mana.” Dila ya ce: “Har da wani rabo ne? Kuma ka ga dai ka ci batsiya yanzu, in dare ya yi ka ci barewa, ka ajiye zomo ka karya kumallo da safe.” Zaki ya ce: “Dila, wa ya gaya maka wannan rabo?” Ya amsa da cewa: “Kan kura shi ya gaya mini, gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.
Daga Ashraf Da Abdulmajid ’ya’yan Antin Funtuwa, 08152073868