Tarihi ya nuna mana a zamanin tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) wanda ya yi wa Janar Muhammadu Buhari juyin mulki a 1985, aka fara lalata tsarin aikin ’yan sanda da kotuna, aka rusa darajar Naira, aka ciyo bashin IMF, aka sayar da kadarorin gwamnati, aka kori ma’aikata, aka dasa bam ga wani dan jarida Dele Giwa ta hanyar wasika.
A lokacin ne aka rusa Nigeria Airways da Nigeria Railways da NITEL da NEPA da NAFCON da Ajaokuta da NDIC – Kamfanin Kera Makamai da sauran masana’antu da noma.
- Muhimman abubuwan da Buhari ya tabo a jawabinsa na sabuwar shekara
- Mutum 12 sun mutu a turmutsitsin wurin ibada a Indiya
A lokacin aka kaddamar da koyar da ilimin jima’i ga yara a makarantu aka shigo da shirin kayyade iyali aka haddasa rashin jituwa a tsakanin ’yan Arewa da Kudu da tsakanin Musulmi da Kirista, aka yi ta yin rikice-rikicen addini har da kashe-kashe a Kaduna da Jos da sauransu har Mai shari’a Karibi Whyte ya yanke wa Janar Zamani Lekwot hukuncin kisa amma gwamnatin ta yi masa afuwa.
A zamanin Janar Sani Abacha ya kafa kwamitin Mai shari’a Pious Okigbo, wanda ya bankado almundahana da Dala biliyan 12.2 na mai a lokacin Yakin Tekun Pasha a zamanin Janar Babangida, ba a sa su a asusun CBN ba.
Janar Babangida ne har wa yau ya soke zaben da ya fi kowane zabe da aka taba yi inganci da adalci da karbuwa ga Musulmi da Kiristocin Najeriya da duniya baki daya, amma ya kawo Earnest Shonekan ba tare da zabe ba don ya wanke kansa.
Da bai samu karbuwa ba ya hada kai da tsohon Shugaban Kasa Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), suka yafe wa Janar Olusegun Obasanjo (mai ritaya) hukuncin da aka yanke masa na daurin rai-da-rai wanda aka mayar shekara 25, suka sa ya shiga jam’iyyarsu ta PDP suka kakaba wa mutane shi, ya zama Shugaban Kasa na farar hula (wanda da Malam Aminu Kano da Cif Obafemi Awolowo suna da rai hakan ba za ta yiwu ba).
An ce sun tsara idan ya yi shekara 4 zai bai wa IBB ya ci gaba. Obasanjo na hawa mulki suka sa aka yi wa manyan hafsoshin sojoji musamman ’yan Arewa da suka taba rike ofishin siyasa kama daga Gwamna, minista da sauransu ritayar dole, ba tare da sun yi laifin komai ba, sai don ana jin tsoron kada su hana ruwa gudu.
Karshenta dai sai da ta kai su IBB sun kai karar Obasanjo wurin su Cif Rotimi Williams da Cif Abraham Adesanya a kan wai sun yi alkawari da shi idan ya yi shekara 4 zai sauka ya ba su. Su kuma da suka kira Obasanjo domin su ji ta bakinsa, da ya je ya nuna musu a matsayinsu na lauyoyi ya roki su duba kundin tsarin mulkin Najeriya da na PDP ko akwai wani tanadi da ya hana wanda ya yi zangon farko ya nemi zango na biyu? Idan sun ce sun yi alkawari ba zai nemi zango na biyu ba, a nuna masa takardar da ya sa hannu a kan haka.
Sannan ya yi musu bayanin cewa, shekara 20 da barinsa mulki, (1979 – 1999) ya zo ya tarar duk dukiyar da ya bari an sace, an ciyo bashi na Dala biliyan 30.
Ya ce ya bar jiragen sama 47 babu ko daya lokacin da ya dawo, ga jiragen kasa da ya bari duk babu su, haka NEPA da NITEL da sauransu. Shi ma a karshe an zargi gwamnatinsa da handame kudin wutar lantarki Dala 16.
Hatta kudade da ake zargin ya kwaci daga hannun IBB da iyalan Sani Abacha da Abdussalami Abubakar da sauransu duk ya hada ya rike maimakon ya sa a cikin asusun gwamnati.
Wadannan mutane fa su ne suka faki idanuwan mutane suka tsara yadda suka yi, suka daddasa yaransu suka zama gwamnonin jihohi 19 na Arewa suka sayar musu da Bankin Arewa (BON) da sauran kadarorin kasar nan.
Ina kudin? Daga nana abubuwa suka ci gaba da tabarbarewa wadansu kalilan suka mamaye komai a kasar ta yadda hatta wakilan Majalisar Dokoki ta Kasa, wadanda ya wajaba su gyara kura-kuran da ake fama da su, don sake mayar da kasar nan kan hanyar kirki sai suka koma ’yan amshin shatan wadancan kalilan din mutane sai yadda aka yi da su.
Dama can an dasa wa mutane neman kudi, kudin ne a gaban mafi yawansu koda na sata ne balle cin hanci da rashawa, ba ruwansu da duk abin da zai biyo baya a nan duniya ko a Lahira.
Alhaji Abdulkarim Daiyabu shi ne Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN) za a iya samunsa ta: 08060116666, 08023106666, 09094744184