✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Qatar 2022: Rikita-rikitar da aka yi kafin amincewa da Gasar Kofin Duniya a Qatar

Tun daga lokacin da Qatar ta shiga neman daukar nauyin gasar Kofin Duniya na 2022, har zuwa yanzu da ake shirin fara gasar ba a…

A ranar 20 ga Nuwamban bana ce za a fara fafata Gasar Cin Kofin Duniya a kasar Qatar da ke yankin Larabawa.

Qatar mai fadin kasa da bai wuce kilomita 12,000 tana cikin kananan kasashe a duniya, sai za a iya cewa karama ce, abokiyar manya saboda tarin arzikinta.

Wani marubucin Mujallar Forbes, Beth Greenfield, ya ce, a game da kasar, “Idan dukiya na nuna karfin kasa, to lallai wuyan Qatar ya isa yanka.”

Haka kuwa kasar ta nuna isa wajen doke kasashen Turai manya ciki har da Amurka wajen samun lasisin daukar nauyin gasar ta bana.

Sai dai duk da cewa a bayyane kasar ta yi duk abin da ya dace wajen samun lasisin dafa Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), daga baya an bankado wasu harkalla da aka yi ta bayan fage.

Kasar, mai kimamin mutum miliyan 2 ce ta farko a yankin Larabawa da ta samu wannan damar, kuma dan Sarkin Hammad bin Khalifa Al Thani mai suna Sheikh Mohammed bin Hamad bin Khalifa Ali-Thani ne ya jagoranci kwamitin neman daukar nauyin gasar.

Shugaban kwamitin ya yi amfani da siyasar cewa yankin Larabawa bai taba samun damar ba, wanda hakan ya sa kasashen yankin suka goya musu baya, sannan ya nuna cewa dama ce domin samun hadin kai tsakanin yankin da Turawan Yamma.

Rikita-rikitar da lamarin ya jawo

Sai dai tun daga lokacin da Qatar ta shiga neman daukar nauyin gasar, har zuwa yanzu da ake shirin fara gasar ba a daina ka-ce-na-ce ba, sakamakon matsalolin da lamarin ya haifar.

Qatar ta fuskanci kalubale da kushe daga ’yan jarida da masu sharhi kan harkokin wasanni da hukomomin kare haddin dan Adam musamman kan tarihin harkar kwallon kafa a kasar.

Dalilan masu kushen sun hada da cewa kasar ba ta taba zuwa Gasar Kofin Duniyar ba, da batun kare hakkin dan Adam da kuma uwa-uba yanayin zafin kasar wanda dole ya sa aka daga lokacin da aka saba gasar zuwa lokaci mai dan saukin zafi.

A ranar 17 ga Nuwamban shekarar 2010 ce Shugaban FIFA na wancan lokacin, Sepp Blatter ya amince da kudurin Qatar na daukar nauyin gasar.

A cewarsa a lokacin, “Yankin Larabawa ya cancanci daukar Gasar Kofin Duniya, amma ba su taba samun dama ba.”

Sai dai matsalolin da suka biyo ba kasar damar daukar nauyin gasar za su iya cewa sun yi doma, da awai din baki daya, domin sai aka dakatar da Sepp Blatter da Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Turai da sauransu saboda samun su da laifin cin hanci har aka hana su shiga harkar kwallon kafa baki daya.

Sai dai daga baya an wanke su daga wasu laifuka.

Zarge-zargen cin hanci

A watan Mayun shekarar 2011, an tuhumi wasu manyan jami’an Hukumar FIFA da cin hanci bayan samun labarin wani mai tonon silili da yake da masaniya a kan yadda Qatar din ta samu doke sauran kasashen wajen samun damar daukar nauyin gasar.

Da yake gabatar da bayani kan lamarin, Lord Triesman, wanda mamba ne a Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila a lokacin, ya ce, Jack Warner, wanda tsohon Shugaban Hukumar FIFA ne, ya nemi a gina musu Cibiyar Ilimi ta Dala miliyan hudu a kasarsa ta Trinidad and Tobago, sannan shi ma Nicolas Leoz, wanda tsohon Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Paraguay ne ya bukaci cin hanci domin bayar da kuri’a.

Haka kuma an zargi Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Ivory Coast, Jacques Anouma da Issa Hayatou na Kamaru da karbar Dala miliyan 1.5 kowannensu domin zabar kasar Qatar, sai dai dukansu sun karyata zargin.

Shugaban Hukumar Kwallo Kafa ta Qatar na lokacin, Mohammed bin Hammam, wanda ya tsaya takarar Shugaban FIFA a can baya shi ma ya shiga cikin zargin.

Bayan zargin da aka masa na hannu wajen cin hancin da aka yin a Qatar 2022, an kuma zarge shi da sayen kuri’ar masu zabe 25 domin zama Shugaban FIFA, wanda hakan ya sa aka dakatar da Hammam daga harkokin kwallon kafa.

Sai dai bayan an dakatar da Jack Warner na Trinidad and Tobaggo, ya ce Sakatare Janar na FIFA na lokacin, Jeroma Vacke ya taba fada masa cewa Qatar sayen dammar daukar nauyin gasar ta yi da kudinta.

Amma hukomimi a yankin sun bayyana cewa babu laifin da suka yi, inda suka ce kawai adawa ake musu.

A wani rahoto da The Sunday Times ta yi, ta bayyana yadda Al Jazeera ta biya FIFA Dala miliyan 400 domin damar nuna wasannin gasar, kwana 21 kafin FIFA ta sanar da Qatar a matsayin kasar da za ta yi dauki nauyin gasar.

Haka kuma jaridar ta bankado wasu kudade da aka ba FIFA, da adadinsu ya kai Dala miliyan 880.

Sai dai FIFA ta ki cewa uffan lokacin da jaridar ta Sunday Times ta bukaci jin ta bakinta, amma rahoton na cikin abubuwan da Hedikwatar FIFA ta yi amfani da su wajen bincike.

A ranar 2 ga Disamban shekarar 2010 ce aka sanar da Qatar a matsayin kasar da za ta dauki nauyin gasar bayan an sha tata-burza.

Sai dai jim kadan bayan sanarwar, a Mayun 2011, Mataimakin Shugaban FIFA na wancan lokacin, Jack Werner aka dakatar da shi, sannan a ranar 10 ga Mayun shekarar aka dakatar da Issa Hayatou na Kamaru da Jacques Anouma na Ivory Coast da Amos Adamu daga Najeriya bayan samun su da laifin karbar cin hancin Dala miliyan 1.5.

’Yancin dan Adam

Wata matsalar da ta jawo kai ruwa-rana ita ce yadda zargin kasar da yin amfani da baki wajen aikin wahala na gina sababbin filayen wasanni, kamar yadda Amnesty International ta sanar.

Haka kuma akwai wani rahoto da ake zargin kasar da azabtar da bakin haure masu shiga kasar daga kasashen Indiya da Pakistan da Sri Lanka da wasu kasashen.

Wani rahoton The Guardian ya nuna cewa daga shekarar 2010 zuwa bana, akalla bakin haure 6,500 ne suka mutu a kasar, sannan mutum 36 daga cikin wadanda suka mutu rasuwarsu na da alaka da aikin gine-ginen shirin daukar nauyin Gasar Kofin Duniyar.

Sai dai da yake mayar da martini kan lamarin, wakilin Ma’aikatar Kwadago na kasar ya karyata zargin, inda ya ce kasar tana kokari sosai wajen kula da ’yan kwadago, duk da ya amince akwai sauran aiki a gabansu.

Yanayin zafin kasar

A ka’ida, ya kamata tuni an kamala Gasar Kofin Duniya ta bana, domin a watan Yuni ko Yuli ake fafata gasar.

Amma Hukumar FIFA ta amince da canja lokacin domin dacewa da yanayin kasar ta Qatar, musamman yanayin zafin kasar mai, inda zafin rana kan kai sama da 43 a ma’aunin Celsius.

Dambarwar sauya lokaci

Sai dai an zargi kasar da karya a farkon lokacin da take neman daukar nauyin gasar, inda ta ce ta shirya tsaf domin samar da filayen wasanni masu na’urorin sanyaya waje wato AC manya da za su magance matsalar zafin.

Yanayin kokarin sauya lokacin gasar ya haifar da kai-komo, inda kasashe suke cewa hakan zai shafi gasanni, musamman manyansu kamar Firimiyar Ingila da La liga da Spain da Serie A ta Italiya.

An so a mayar da gasar Janairu ko Fabrairu, nan ma aka ce za ta hade ta Gasar Olympic na bazara.

Sannan aka ce watan Nuwamba ko Disamba, wanda nan ma aka ce zai iya shafar shirin bikin Kirsimeti.

Hukumar Gasar Firimiyar Ingila ta nuna rashin amincewarta cewa zai shafi gasar kasar.

Matsayar amfani da Nuwamba zuwa Disamba sai da ta haifar da ce-ce-ku-ce a FIFA, inda Sakatare-Janar na hukumar na lokacin, Jerome Valcke ya ce sun amince da watan, shi kuma Mataimakin Shugaban hukumar na lokacin, Jim Boyce ya ce ba a yi hakan ba saboda Kirsimeti.

Daga cikin kasashen da suka fi nuna damuwa a kan matakin, akwai Ingila da a lokacin ta yi barazanar zuwa kotu saboda yadda lamarin zai shafi Firimiyar Ingila, da Hukumar Kwallon Kafa ta Australia da ta ce FIFA za ta biya ta diyya.

Bayan tata-burza da aka sha, wani mamba a Hukumar FIFA na lokacin, Theo Zwanziger ya fito ya bayyana cewa, “An tafka kuskure,” wajen ba Qatar damar daukar nauyin gasar.

Daga baya dole aka mayar da gasar watan da muke ciki, wanda hakan ya sa ake kallon kasar a matsayin ’yar lele ganin yadda hakan ya shafi gasannin kwallon kafa na kasashe, musamman Turai.

Shan giya da matsayar masu luwadi da madigo

Qatar kasa ce ta Musulunci, wadda shan giya haramun ne.

Sai dai kuma kamfanonin giya suna cikin masu daukar nauyin gasar ta Kofin Duniya, wanda hakan ya sa aka shiga fargabar yadda za ta kaya.

Da yake amsa tambaya kan hakan, Shugaban Kwamitin gasar na Qatar, Hassan Abdullahi al Thawed ya ce za a tanadi wasu wajaje na musamman ga wadanda suka shigo kasar domin kallon gasar da za a iya zuwa a sha giya.

A game da batun ’yan madigo da masu luwadi wadanda haramun ne a kasar, inda a kan daure wadanda da aka kama da laifin a kurkutu har na tsawon shekara bakwai zuwa tara, a ranar 8 watan Disamban 2020, kasar ta sanar da cewa a shirya take ta yi amfani da sharudan da FIFA ta gindaya.