✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

QATAR 2022: ‘FINAL’ Tsakanin Ajentina Da Faransa

Daga karfe 4:00 na yamma agogon Najeriya, yau Lahadi Aminiya za ta kawo muku rahotanni kai-tsaye daga Wasan Karshe na Gasar Cin Kofin Duniya na…

Daga karfe 4:00 na yamma agogon Najeriya, yau Lahadi Aminiya za ta kawo muku rahotanni kai-tsaye daga Wasan Karshe na Gasar Cin Kofin Duniya na 2022 da ke gudana a kasar Qatar.

Za a buga wasan karshen ne tsakanin tawagar kasashen Faransa da Ajentina a filin Wasa na Lusail Iconic mai daukar mutum 80,000, wanda kuma shi ne filin wasa mafi girma a kasar Qatar.

Kowanne daga manyan ’yan wasa da kuma kasashensu na neman kafa tarihi, bayan shafe mako hudu kasashe 32 suna fafatawa a wasanni 64 na gasar.

Gasar Qatar 2022 wadda ita ce karo na 22 a tsawon shekara 92 na tarihin gasar, ta zo da abubuwan ban mamaki kuma ita ce ta farko a yankin kasashen Larabawa.