A bana dai duniyar wasanni za ta shiga hidima yayin da wasu manyan gasanni za su gudana.
Akwai gasanni irinsu kwallon kafar mata da wasannin motsa jiki na guje-guje da tsalle-tsalle na duniya da kwallon kwando da wasan kankara da za su gudana a bana.
- NAJERIYA A YAU: Manufofin ’Yan Takarar Gwamnan Kano A Zaben 2023
- Buhari ya yi tir da kisan ’yan sa-kai a Katsina
Kakar wasanni ta 2023 za ta nishadantar da masu kallo da gasanni iri-iri kuma tuni ma aka fara wasu.
Gasar Kofin Duniya na Kungiya (Club World Cup)
Real Madrid za ta fafata da Al Ahly a daf da karshe a Club World Cup ranar 8 ga watan Fabrairu da Morocco ke karbar bakunci.
Ranar Asabar kungiyar Masar ta yi nasara a kan Seattle Sounders da ci 1-0, kuma Mohamed Afsha ne ya ci kwallon saura minti biyu a tashi daga wasan.
Da wannan sakamakon Al Ahly, wadda Marcel Koller ke jan ragama za ta fuskanci Real Madrid ranar Laraba a Rabat.
Ita kuwa kungiyar Saudi Arabia, Al Hilal ta yi nasara a kan Wydad Casablanca ta Morocco a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1 ranar Asabar 4 ga watan Fabrairu.
Al Hilal ta kai daf da karshe ke nan da cin 5-3 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Da wannan sakamakon, Al Hilal za ta fuskanci Flamengo a daya wasan daf da karshe ranar Talata 7 ga watan Fabrairu.
Ranar 11 ga watan Fabrairu za a buga neman mataki na uku tsakanin wadda aka doke ranar Talata da wadda ta yi rashin nasara ranar Laraba.
A dai ranar ta Asabar 11 ga watan Fabrairu za a buga wasan karshe a filin Moulay Abdallah tsakanin wadda ta yi nasara ranar Talata da Laraba.
Gasar Kofin Duniya ta Kwallon Kafa ta Mata
Gasar cin kofin kwallo kafan duniya ta mata ba ta taba kasancewa a irin wannan lokaci ba.
Daga ranar 20 ga watan Yuli zuwa 20 ga Agusta, kungiyoyi 32 ne za su halarci gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a Ostiraliya da New Zealand a karon farko.
Tawagar Jamus na son sake samun nasarar lashe gasar bayan rashin nasara a wasan karshe na Gasar Kofin Nahiyar Turai.
Gasar Super Bowl
A ranar 12 ga Fabrairu, za a gudanar taron wasanni mafi girma a duniya wanda zai gudana a Arizona na Amurka.
Shi ne taron NFL karo na 57, kamar kullum, zai kasance mai girma – cikin tarukan motsa jiki.
Abin da ya rage kawai ga magoya baya a cikin jihar hamadar Amurka: Cardinal Arizona, ita ce kungiya mai masaukin baki, mai yiwuwa ba za ta rasa wasannin share fage na wannan kakar ba.
Tseren Keke na Tour de France
Gasar tseren keke karo na 110 ta duniya za ta fara a 1 ga watan Yuli a Bilbao da ke Arewacin Spain, kuma bisa ga al’ada za a kare ranar 23 ga Yuli a Champs-Élysées a birnin Paris.
Abin daukar hankali a 2023 zai zama gagara- badau: a kan hanyar mai tsawon kilomita 3404, masu tseren keken za su haye nau’ukan tsauni har 30 a cikin mafi girman nau’ukan – don zama sabon zakaran tseren keke.
Kwallon Gora a kan kankara ta duniya
Rasha, daya cikin kungiyoyin wasan kwallon gora na kan kankara masu karfi, ba za su halarci gasar a bana ba.
Gasar za ta gudana ne a Tampere na kasar Finland, da kuma Riga, babban birnin Latvia, a watan Mayu.
Jamus na son yin fiye da yadda ta yi a 2022 lokacin da Jamhuriyar Chek ta fitar da ita a wasan kusa da na karshe.
Sai dai kungiyar ta DEB na cikin rudani bayan da koci Toni Söderholm ya raba gari da ita.
Wasannin guje-guje da tsalle-tsalle
Daga ranar 19 zuwa 27 ga watan Agusta, Budapest babban birnin kasar Hungary zai kasance cibiyar dukkan masu sha’awar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle.
Kimanin ’yan kallo 37,000 za su iya zama a cibiyar wasannin motsa jiki da aka gina musamman domin gasar cin kofin duniya.
’Yan wasan za su nuna bajinta a gudu da tsalle don samun lambobin yabo a jimillar fannoni 49.
Gasar tseren kankara ta duniya
Daga 6 zuwa 19 ga Fabrairu, kwararrun ’yan tseren kankara za su fafata don samun lambobi na gasar cin kofin duniya a kan tsaunin Courchevel da Méribel na yankin Alps na kasar Faransa.
Babban abun kallo daga Jamus shi ne Thomas Dreßen, wanda ya koma gasar cin kofin duniya bayan dogon rauni da ya yi, da kuma kwararriya Lena Dürr.
Kofin Kwallon Hannu na Duniya
Daga ranar 11 zuwa 29 ga watan Janairu, kungiyoyin kwallon hannu 32 da suka fi fice a duniya za su fafata a Poland da Sweden.
Ba kamar yadda aka yi a Masar shekaru biyu da suka gabata ba, kungiyar Jamus za ta so sake kaiwa matakin wasan karshe don lashe gasar.
Masu rike da kambun su ne Denmark, wadanda suka doke Sweden a wasan karshe na 2021.
Wasannin Olympics na musamman
Gasar Olympics ta musamman ita ce kungiyar motsa jiki mafi girma a duniya ga mutanen da ke da nakasar kwakwalwa.
Za a yi wasannin bazara a Berlin a watan Yuni.
Ita ce gasar Olympics ta musamman ta kasa da kasa ta farko a kasar Jamus.
Ana sa ran kusan ’yan wasa 7000 daga kasashe 170 za su halarta.
An riga an yi wasannin hunturu a watan Janairu a Bad Tölz a jihar Bavaria.
Kofin Duniya na kwallon Kwando
Za a gudanar da gasar kwallon kwando ta duniya daga ranar 25 ga Agusta zuwa 10 ga Satumba a Philippines da Japan da Indonesia.
Har ila yau, tawagar Jamus a can tana fata – tare da daukan taurarin NBA a kusa da Dennis Schröder.
Yin aiki mai kyau kuma zai zama abu mai muhimmanci saboda manyan kungiyoyi bakwai sun cancanci kaiwa zuwa gasar Olympics ta 2024 a Paris.
Kofin Duniya na Cricket
Gasar cin kofin duniya ta Cricket za ta gudana ne a cikin kaka a kasar da ba wasu wasanni banda wasan Cricket.
Indiya ce ke karbar bakoncin gasar karo na 13 a karo na hudu.
“Maza sanye da rigunan kalar bula” suna da sha’awar lashe gasar duniya ta uku bayan 1983 da 2011.
Ingila ce ke rike da kofin. Tun da farko, an shirya gudanar da gasar a watan Fabrairu, amma aka dage ta saboda COVID-19.
Gasar Kwallon Kafa ta Asiya
Tun da farko ya kamata a gudanar da gasar a kasar China a watan Yuni da Yuli, amma China ta fasa karbar gasar saboda annobar corona.
Sabbin masu masaukin baki dai sun hada da Qatar mai rike da kofin gasar, wanda cikin mamaki ta doke Japan a wasan karshe na 2019.
A saboda tsananin zafin hamada a rani, gasar cin kofin Asiya ta 2023 tabbas ba za ta gudana ba har sai Janairun 2024.
Wasannin sojoji nakasassu
An fara gudanar da taron wasanni na nakasassun sojoji tun daga shekarar 2014.
Amma karo na shida zai gudana ne daga ranar 9 zuwa 16 ga Satumba a Düsseldorf.
Kungiyoyin za su fafata don samun lambobin a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da wasan harbi da wasan kwale-kwale na cikin gida, da daga nauyi da tseren keken da wasan kwallon kafa da wasan ninkaya da zari ruga na guragu.