Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin ya sanar da yiwuwar ci gaba da daina tura iskar gas ga kasashen Turai ta bututun Nord Stream 1 da kasarsa ke wa garambawul.
Putin ya sanar da haka ne kasa da awa 48 da sake bude bututun, wanda ke tura wa kasashen Turai makamashin iskar gas kai-tsaye ta kasar Jamus — ranar Alhamis.
- Mutum 189 sun kamu da Kwalara a kananan hukumomi 20 a Kano
- Mako 2 da Buhari ya bai wa Ministan Ilimi ba zai yi aiki ba idan… — ASUU
- Yajin aiki: Sai mun ga abin da ya ture wa Buzu nadi — ASUU
Ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da Shugaban Kasar Turkiyya Recept Teyep Erdowan, a lokacin ziyarar aiki da suka kai wa takwaransu na kasar Iran Ebrahim Raisi a ranar Talata.
Hakan kuwa na zuwa ne bayan a watan Yuni kamfanin iskar gas na Rasha, Gazprom, ya rage adadin iskar gas din da yake ba wa kasashen Turai da kashi 60 cikin 100.
Bututun Nord Stream 1, wanda a halin yanzu Rasha ta rufe domin yi masa wa garambawul na shekara-shekara shi ne hanya daya mafi girma da take amfani da ita wajen biyan bukatun nahiyar Turai na makamashin.
Nord Stream 1 na da karfin tura kyubit mita miliyan 167 na makamashin a kowace rana, amma a watan Yuni, Gazprom ya rage adadin da yake turawa zuwa miliyan 67.
Putin ya yi gargadin cewa muddin ba a dawo wa kasarsa da injinan tura makamashin da ta kai gyara kasar Kanada ba, adadin na iya raguwa zuwa miliyan 33 nan a kwana 10 masu zuwa.
Tun bayan mamayar da Rasha ta fara kai wa makwabciyarta Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu, 2022, hankalin duniya ya fara komawa kan makomar katafaren bututun.
Hakan kuwa na da nasaba da yunkurin kasashen Turai na karya lagon Putin da kuma ruguza tattalin arzikin Rasha, jagaba a arzikin iskar gas.
Sai dai kuma, kasahen nahiyar sun dogara ne da Rasha wajen samun akalla kashi 60 na iskar gas da suke bukata.
Rasha dai ita ce kasar da ta fi arzikin iskar gas a duniya, a bangaren danyen mai kuma ita ce ta biyu wajen bayan kasar Saudiyya.