✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PSG na biyan Neymar fiye da Naira Miliyan 1 a kowace sa’a – Bincike

Wata kafar watsa labarai da ke Jamus Der Speigel a wani binciken da ta yi game da albashin dan kwallon da ya fi kowanne tsada…

Wata kafar watsa labarai da ke Jamus Der Speigel a wani binciken da ta yi game da albashin dan kwallon da ya fi kowanne tsada a duniya dan asalin Brazil Neymar ta nuna yanzu haka kulob din PSG na Faransa yana biyan sa Naira Miliyan 1 da dubu 700 ne a kowace sa’a daya a matsayin albashi.

Kamar yadda binciken ya nuna, ta ce dan kwallon a kullum yana samun Yuro dubu 100 ne kwatankwacin Naira Miliyan 42 ko kuma Yuro dubu 4 kwakantwacin Naira miliyan 1 da dubu 700 a kowace sa’a daya.

Haka kuma dan kwallon an nuna yana karbar albashin Yuro miliyan 3 ne kwatankwacin Naira Biliyan 1 da dubu 300 a wata kamar yadda sabon kwantaragin da ya sanya hannu a kulob din na PSG ya nuna.

Kamar yadda kafar watsa labaran ta samo wannan bayani bayan ta yi bincike mai zurfi, an nuna Neymar, dan kimanin shekara 25 zai karbi albashin Yuro Miliyan 36 ne kwatankwacin Naira Biliyan 16 a shekara.

Rahoton ya kara da cewa, kulob din PSG ya amince zai biya na FC Barcelona da ke Sifen zunzurutun Fam Miliyan 214 kwatankwacin Naira Biliyan 104 a tsawon shekara biyar da zai kwashe a kulob din PSG kamar yadda yarjejeniyar da suka kulla game da cinikin dan kwallon ta nuna.

Haka kuma kididdigar ta nuna Neymar yana karbar Yuro 66 ne kwatankwacin Naira dubu 28 a kowane minti daya a matsayin albashi.

Jama’a da dama ba su san ainihin albashin dan kwallon zai karba ba tun bayan  da ya canza sheka daga FC Barcelona zuwa na PSG amma yanzu jaridar ta Jamus kamar ta fasa kwai ne game da yawan kudin da Neymar yake karba a matsayin albashi.