✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pogba da Pogba za su hadu a gasar Europa

Kulob din Manchester United na Ingila zai hadu da na Saint-Etienne na Faransa a wasa zagaye na biyu na gasar cin kofin Turai mataki na…

Kulob din Manchester United na Ingila zai hadu da na Saint-Etienne na Faransa a wasa zagaye na biyu na gasar cin kofin Turai mataki na biyu da aka fi sani da Europa. Kenan, Paul Pogba, dan kwallon Manchester United zai hadu da Yayansa Florentin Pogba da ke buga wa kulob din Saint Etienne kwallo.

A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar shirya kwallo a Nahiyar Turai (UEFA) ta fitar da jadawalin yadda wasannin za su kaya a matakin zagaye na biyu inda ta hada kungiyoyin biyu. A ranar 16 ga watan Fabrairun 2017 ne za a fara wasan farko a filin wasa na United da ake kira Old Trafford sannan bayan mako daya United za ta yi tattaki zuwa Faransa don yin wasa zagaye na biyu.
Jim kadan bayan an fitar da jadawalin ne sai rahotanni suka nuna Paul Pogba ya barke da dariya bayan ya lura da yadda aka hada kulob dinsa da na Yayansa Florentin a wasa zagaye na biyun.
Daga nan ne kafofin watsa labarai a sassan duniya suka shiga yin sharhi game da yadda ’yan kwallon wa da kani za su hadu da juna a gasar a karon farko.
Florentin dan kimanin shekara 26 da haihuwa, ya ba kaninsa Paul Pogba tazarar shekara uku.
A halin yanzu Paul Pogba ne dan kwallo mafi tsada a duniya bayan ya canza sheka daga kulob din Jubentus na Italiya zuwa na Manchester United da ke Ingila a kan zunzurutun Fam miliyan 89 ko Yuro miliyan 100.