✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PIA: Najeriya ta yi asarar Dala biliyan 50 saboda jan kafa

Rashin aiwatar da dokar man fetur ya ja wa Najeriya babbar asara, inji Buhari.

Najeriya ta yi asarar da yawanta ya kai Dala biliyan 50 saboda tafiyar hawainiyar shekara 10 da aka yi wajen aiwatar da Dokar Man Fetur (PIB).

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce asarar zuba jarin kudaden da kasar ta yi a tsawon shekara 10 da rashin tabbas ya dabaibaye aiwatar da dokar ya haifar, ya kawo tsaiko ga ci gaban tattalin arzikin kasar.

Ya zargi rashin mayar da hankalin gwamnatocin baya na samar da sauye-sauyen da suka dace, duk da cewa “Gwamnatocin na gaba sun fahimci dacewar a sauya bangaren man fetur din kasar nan daidai da harkokin kaswancin duniya na zamani.

“Amma duk da haka ba su mayar da hankali ba domin ganin hakan ya tabbata; Hakan kuma ya kawo wa bangaren tsaiko da kuma rashin bunkasar tattalin arzikin kasarmu.

“A shekara 10 da suka wuce Najeriya ta yi asarar da kimarta ta kai Dala  biliyan 50 saboda rashin tabbas din da rashin aiwatar da dokar ya haddasa,” inji shi.

Da yake bayani a ranar Laraba yayin sanya hannnu a kan  dokar da ta zama PIA a yanzu, Buhari ya ce dokar ta kawo karshen rashin tabbas din da bangaren man fetur din Najeriya ke ciki.

A cewarsa hakan zai kawo sauye-sauyen da suka dace a bangaren, wanda hakan na daga cikin manufofin gwamnatinsa.

“A matsayin kasar da ta dogara da albarkatun man fetur domin bunkasa wasu bangarori, banfaren man kasar na aiki da dokar a aka yi sama da shekara 50 da suka wuce; Dokar Fetur ta 1969 da sauran tsoffin dokoki.”

Amma sanya hannu a kan PIA ta 2021 ta bude kofar bankasar bangaren da zai jawo masu zuba jari da ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

Sylva zai jagoranci aiwatarwa

Buhari ya ce Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Timipre Sylva, ne zai jagoranci aiwatar da sauye-sauyen.

Ya kuma umarci hukumomin gwamnati su ba ministan duk hadin kan da ya dace domin tabbatar da tsare-tsaren na inganta tattalin arziki.

Buhari ya kuma fara daukar matakan aiwatar da PIA din inda ya kafa kwamitin aiki da cikawa karkashin jagorancin Ministan, ya kuma ba su wa’adin wata 12, kuma za su rika sanar da shi halin da ake ciki a-kai-a-kai.