Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya lashe kambun ta wanda ya fi kowa shahara a Najeriya a 2022.
Gasar dai tana samun sahalewar Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da wata kungiyar shirya fina-finan yankin, kuma za a ba da lambar girmamawar ga dukkanin wadanda suka samu nasara a cikin gasar a watan Nuwamban 2022 a Abuja.
- ’Yan bindiga sun yi kisa, sun sace mutane da dama a kasuwar Kogi
- Labarin kudurin sauya wa Kaduna suna zuwa Zazzau na kanzon kurege ne — Sanata
Wannan dai shi ne karo na hudu da kungiyoyin suka shirya makamanciyar wannan gasar, kuma ana shiryata ne a karshen kowacce shekara.
An kammala gasar ce bayan shafe tsawon sati biyu ana kada kuri’a, kuma wani gidan Talabijin mai suna Igbere TV ne ya shirya ta.
Kazalika, ’yan Najeriya na gida da ma na ketare ne suka kada kuri’a gasar ta intanet.
An dai fara tattara kuri’un ne tun daga ranar daya zuwa 14 ga watan Agustan 2022, inda sakamakon ya nuna Obin ya samu kuri’a 2,428,403, sai mai biye masa Shugaban gubgun kamfanonin BUA, Abdulsamad Isyaka Rabiu da ke da kuri’u 1,124,172.
Wanda ya samu nasarar zamowa na uku shi ne fitaccen mawakin Kudancin Najeriya David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido wanda ya sami kuri’a 881,766.