Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, ya yi ganawar sirri da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed.
Taron ya gudana ne a Ramat House da ke Bauchi, sai dai ba a bayyana manufar taron ba.
- Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai
- ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Abuja
Obi ya isa Filin Jirgin Sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Alhamis, inda Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Auwal Mohammed Jatau, ya tarbe shi.
Rahotanni sun nuna cewa Obi da Gwamna Mohammed sun tattauna wasu batutuwa da suka shafi babban zaɓen 2027 da kuma makomar siyasarsu.
Wannan ganawa ta wakana ne a daidai lokacin da ’yan siyasa ke shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Obi ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, wanda tsohon gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu na jam’iyyar APC, ya lashe.