Jam’iyyar PDP mai mulki a Jihar Bauchi ta fara shirye-shiryen gudanar da sabon zaben fitar da dan takarar gwamna a Jihar.
PDP ta yanke shawarar sake gudanar da sabon zaben fid da gwani na gwamna, bayan da dan takarar jam’iyyar Ibrahim Kashim Mohammed, ya yi murabus.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Yayanuwa Zainabari ne ya tabbatar da lamarin yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Bauchi.
Ya ce “Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Bauchi Barista Ibrahim Muhammad Kashim, ya janye takararsa don kashin kansa, tun da ya sauka da kansa jam’iyyar ba ta da wani zabi illa ta samu wanda zai maye gurbinsa ta hanyar sabon zaben fiidda gwani.”
Kashim dai ya yanke wannan shawarar ne bayan da gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, ya gaza samun tikitin takarar neman tikitin takarar shugaban kasa a PDP.
Yayanuwa ya ce jam’iyyar na bin tsarin ne kamar yadda dokar jam’iyya da kuma dokokin zabe suka tanada.
“Muna bin tsarin kuma za mu gudanar da sabon zaben fidda gwani na gwamna”.
Kakakin PDP ya ce gwamna Bala ya nemi tikitin takarar shugaban kasa ne bisa kiraye-kirayen da ‘yan Najeriya daban-daban da masu kishin kasa suka yi masa, ya amsa kiran da suka yi masa a yanzu al’ummar Jihar Bauchi na son ya tsaya takara karo na biyu.
“Wannan ya sa jama’ar jihar suka yanke hukunci, kuma duk abin da jama’a suka yanke shi ne za a yi, don gwamna mutum ne mai sauraro kuma mai amsa kiran al’ummarsa.”