Jam’iyyar PDP ta yi watsi da tsarin karba-karba wajen tsayar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, inda ta bai wa dukkanin manema takarar damar gwada bajintarsu wajen samun tikitin tsayawa jam’iyyar takara.
Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, sun dauki matsayi daban-daban kan batun fitar da dan takara daga kowacce shiyya, inda shugaban jam’iyyar na kasa Iyioricha Ayu ya ce dole ne a samar da sauyi kan wancan tsarin.
- Aljeriya ta yi wa fursunoni 1,000 afuwa albarkacin Ramadan
- Karatun allo ne mafi dacewar haddar Alkur’ani —Malam Nazir Kano
A makon da ya gabata ne dai aka kammala taron kwamitin zartaswa na jam’iyyar PDP a karkashin jagorancin gwamna Samuel Ortom, na jihar Benuwe ba tare da samar da mafita kan matsalar ba.
Sai dai a yayin zaman da ta gudanar aranar Talata, kwamitin wanda ya kunshi mutum 37, ya sake shafe sama da sa’o’i uku, inda aka yanke shawarar yin watsi da tsarin karba-karba da aka san jam’iyyar a kai tun fil-azal.
Sai dai wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa, kwamitin ya tabbatar da cewa duk da cewa shiyya-shiyya na cikin kundin tsarin mulkin jam’iyyar, amma ta yanke shawarar barin tikitin takarar ga mai rabo.
Majiyar ta ce “Tun wajen wata shida kafin fara sayar da fom din neman takara, jam’iyyarmu ta yi kokarin warware matsalar tsarin karba-karba, kuma kowanne dan takara yana sane da hakan.”