Rikici ya kaure tsakanin jam’iyyar adawa ta PDP da APC mai mulki kan sabbin manufofi tara da Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta sa a gaba.
A ranar Talata Buhari ya bayyana jerin abubuwan da gwamantinsa za ta ba wa muhimmanci a shekara ukun da suka rage masa, da suka hada da samar da ingataccen ilimi da kula da lafiya da wutar lantarki da rage talauci da sauransu.
Jam’iyyar PDP a wani sako da Sakataren Yada Labaranta, Kola Ologbondiyan ya fitar ta ce shekaru bayar bayan hawa mulkin Buhari bai daina alkawarun ‘da ba a cikawa’, alhali takwarorinsa a wasu kasashe ke bajekolin nasarorinsu.
Ologbondiyan ya ce akwai yaudara a cikin sabbin maufofin Buharin wanda bai cika alkawuran zaben da ya yi a wa’adinsa na 2015 zuwa 2019 ba na yaki da rashwa da farfado da tattalin arziki da kuma samar da tsaro”, inji sanarawar.
– Alkawuran da Buhari da APC suka yi
Ya ce, “Ya kamata duniya ta tuna cewa Shugaban Kasa da jam’iyyarsa ta APC sun yi wa ’yan Najeriya romon baka suka zabe su amma da suka ci zabe sai suka juya wa alkawuran baya.
“Shugaba Buhari da APC sun yi alkawarin biyan matalauta albashin N5,000 da samar da dimbin ayyuka da gidaje kyauta da kuma alawus a duk wata ga matasan da suka kammala yi wa kasa hidima.
“Sun kuma yi alkawarin rage farashin mai da farfado da matatun mai tare da mayar da darajar Naira daidai da na Dala da sauran alkawuran da a yaunzu sun zama tamkar kawalwalniya.
“Bayan hawa Mulki, Shuga Buhari ya rage alkawuran nasa suka koma guda uku da suka hada da yaki da ta’addanci da samar da tsaro, yaki da rashawa da farfado da tattalin arziki”.
– Shuru ake ji har yanzu
“Sanin kowa ne cewa Shugaba Buhari ya gaza a duk alkawuran guda uku.
“A shekara biyar na mulkin Buhari matsalar tsaro ta tsananta fiye da kowane lokaci da ’yan fashin daji, masu tayar da kayar baya da masu garkuwa da mutane a biraen da kauyuka, ciki har da Jihar Katsina, mahaifarsa, alhali shi da ya yi alkawarin na zaune cikin tsaro da walwala a Fadar Shugaba Kasa”, inji PDP.
– PDP ba ta da bankin Magana -APC
A martaninsa, Mataimakin Kakakin APC na Kasa, Yekini Nabena ya ce yanzu “wala-wala a tattalin arziki da rashin kammala ayyuka da cuwacuwa” da suka yafu a zamanin PDP sun kau.
A matsayin PDP na jam’iyyar adawa a yanzu, abin kunya ne ta rika ambaton munanan abubuwan da ya ce gwamnatin PDP ta yi na yada cuwacuwa.
“Bata lokaci ne magana da PDP bayan gwamantinta ta gaza yanzu kuma rasa alkibla a matsayin jam’iyyar adawa.
“Abin da ya fi fitowa shi ne, kar a kara sakawa PDP ta mulki kasar nan.
– Me Gwamnatin Buhari ta yi?
Ya ci gaba da cewa a Gwamnatin Buhari ta APC Najeriya ta zama kasa mafi karfin tattalin arzikin a Afirka an yi tsarin daidaita farashin mai sannan kasar na ciyar da kanta tare da samun ci gaba.
“Shin har yanzu rashawa ta tsayu da kafarta? A’a. Shin ana ba da bayanan kudaden da ake kashewa kan ayyuka? Eh. Kara saukaka wa ’yan kasashen duniya yin kasuwanci da muka yi ya jawo masu zuba jari da cin riba a Najeriya? Eh.
“Mu dai za mu kara hada kai da ’yan kasa nigari mu taimaka domin samun nasara a bangarorin da Shugaba Buhari ya ba wa muhimmanci”, inji APC.
– Abubuwan da Buhari ya ba wa muhimmanci
Bangarorin da Shugaba Buhari ya ce zai ba wa muhimmanci su ne samar da ilimi mai nagarta da wutar lantarki tsayayya da kuma kiwon lafiya managarci da rahusa.
Akwai kuma samar da tattalin arziki mai dorewa da inganta masana’antu da kuma ba wa jama’a dama da yaye talauci.
Ya ce zai kuma inganta sha’anin noma domin samar da wadataccen abinci har a rika fitarwa da kuma samar da ingantaccen sufuri.
Uwa uba zai bullo da hanyoyin yakar rashawa da kuma inganta harkar tsaro.