Shugabannin babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun sha alwashin kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki a 2023.
Shugabannin PDP sun bayyana haka ne a wajen rantsar da sabbin ’yan kwamitin gudanarwarta a Abuja a ranar Juma’a.
- Sudan: An kashe mutum 138 a sabon rikicin kabilanci a Darfur
- Buhari ya tura tawaga ta musamman zuwa Sakkwato da Katsina
PDP ta zargi APC da gazawa wajen inganta rayuwar ’yan Najeriya, don haka ya kamata a sauya ta.
Sabon shugaban jam’iyyar PDP, Sanata Iyrochia Ayu, ya soki APC da cea ta gaza alkawuran da ta yi na kyautata rayuwar ’yan Najeriya.
Ayu ya ce tattalin arzikin Najeriya ya durkushe, tsaro ya tabarbare har an shiga yanayin da a wasu sassan kasar nan ’yan ta’adda ke cin karensu babu babbaka.
Kazalika ya sha alwashin cewa idan PDP ta karbi mulki komai zai daidaita.
Amma APC ta sha musanta zargin da ake mata na zaga cika alkawuran da ta daukar wa talakawa.
Sabbin shugabannin PDP dai sun karbi jagorancin jam’iyyar ne a daidai lokacin da rikicin cikin gida ya dabaibaye jam’iyyar, musamman ma zargin da ake yi cewa gwamnoni sun kwace iko da jam’iyyar, don haka sabbin shugabannin ma watakila su kare a ’yan amshin-shata.
Amma sabon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na yankin Arewacin Najeriya, Umar Iliya Damagun, ya ce sun shirya kwace mulki a 2023.
Wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar sun yi fatan alheri ga sabbin shugabannin.
Senata Iyorchai Ayu dai shi ne shugaban jam’iyyar PDP na kasa na 16, idan aka hada lissafi da mutum biyar da suka riki mukamin a matsayin riko.
Bincike ya nuna cewar dukkan shugabannin PDP da suka rike jam’iyyar ta hanyar zabe, ba su taba kammala wa’adinsu ba sakamakon rikicin cikin gida.