✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta lashe ƙananan hukumomi 15 a zaɓen Filato

Sauran ƙananan hukumomi guda biyun da ake jiran isowar sakamakon zaɓen su, sune Pankshin da Langtang ta Arewa.

Hukumar Zaɓe ta Jihar Filato (PLASIEC) ta sanar sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin jihar, da ta gudanar a ranar Larabar nan da ta gabata.

Sakamakon zaɓen, ya nuna cewa Jam’iyyar PDP ta lashe ƙananan hukumomi 15 daga cikin 17 da ke jihar.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, a ranar Alhamis hedikwatar hukumar da ke Jos, shugaban hukumar zaɓen Mista Plangji Daniel Cishak ya bayyana cewa ƙananan hukumomin da jam’iyyar ta PDP ta lashe su ne Mikang da Shendam da Bassa da Riyom da Jos ta Kudu da Jos ta Gabas da Kanam da Qua’an Pan da Langtang ta Kudu.

Sauran sune Barkin Ladi da Jos ta Arewa da Kanke da Bokkos da Wase da kuma Mangu.

Shugaban hukumar zaɓen, ya yi bayanin cewa sauran ƙananan hukumomi guda biyun da ake jiran isowar sakamakon zaɓen su, sune Pankshin da Langtang ta Arewa.